Muhammad S Tomo

Muhammad S Tomo

Share

Public Awareness

28/06/2026

Tarihin Imam (Ajtf) Fassarar Hausa - 2

28/06/2026

Duk wanda yake ɗaukar ƙananan masifu a matsayin manya, Allah zai jarabce shi da manyan masifu.

Inji Amirul Mu’uminin (a.s)
Nahjul Balagha

Muhammad S Tomo ✍🏽

27/06/2026

KU UMARCI IYALAN KU MATA !

Wani abu da ya k**ata Iyaye da kuma “Yan uwa maza ya k**ata su lura da shi kuma su tarbiyantar da makusantansu Mata shine saka Hijabi da Muhimmancinsa gare su da kuma Addinin su .

Domin a Dabi’a ko mu ce yadda Allah (T) ya Halicci mata mutane ne masu son Kyau ,Kwalliya da kuma burge wanin su .

Saboda haka ne zaka ga Iya rufe jikinsu abu ne da ke yi musu wahala ba wai don basu san addini ya ce a saka ba ,A’a ! Musamman ma ace sun saka wani abu da suke ganin yayi kyau ko gwanin burgewa .

Idan muka duba Ayoyi da dama a kur’ani zamu ga Idan zasu yi magana da mata kan Hukunci sukan ce kuyi kaza ku bar kaza ne ,Yayin da ayar Hijabi Allah ke cewa Manzon Tsira (S)kacewa Matanka da “Yayanka ………….

Wannan kadai zai iya nuna maka Yadda Al’amarin saka Hijabi ko muce Rufe Jikin mace yake Aiki da yake Bukatar Tsayuwar ku Mahaifa ,Iyaye da “Yan uwa kan Matayen ku .

Muna Fatan Allah ya bamu Ikon Sauke Nauyin da ke kan mu ya kara mana Riko da Umarnin sa mai dadi gare mu da Akasin sa .

Muhammad S Tomo ✍🏽

27/06/2026

Ciki shi ne mazaunin cututtuka, kuma rage cin abin da ke cutarwa da kiyaye abinci shi ne asalin magani. Ba a samun lafiya idan mutum yana da yawan kwaɗayin cin abinci.

Inji Amirul Mu’uminin (a.s)
Bihar J 59 Shafi na 75

Muhammad S Tomo ✍🏽

26/06/2026

Jiya Kenan Yayin gudanar da Muzaharar Ashura a Birnin Qom mai tsarki

Muhammad S Tomo

23/06/2026

KWANA -30 RANA TA -14

Nasara a Lokacin Rayuwar Jagora ko Har Bayan Jagora ?

23/06/2026

Idan Allah Ya ta da mumini daga kabarinsa, wani sura ko halitta mai k**a da mutum zai fito tare da shi yana tafiya a gabansa. Duk lokacin da muminin ya ga wani abun firgici da tsananin abubuwan Ranar Alƙiyama, wannan halittar za ta ce masa:

Kada ka firgita, kada kuma ka yi baƙin ciki. Ina maka bushara da farin ciki da karamci daga Allah Maɗaukaki.

Sai muminin ya ce masa:‘Allah Ya rahamshe ka… Wane ne kai?’

Sai ya amsa da cewa:‘Ni ne farin cikin da ka kasance kana shigarwa cikin zuciyar ɗan’uwanka mumini a rayuwar duniya.’

Inji Imam Sadik (a.s)
Al Kafi J 2 Shafi na 190

Muhammad S Tomo ✍🏽

22/06/2026

Kayi Aiki (nema) Domin rayuwar ka Kamar ba zaka barta (mutu) ba , Kuma kayi Aiki domin lahirar ka Kamar Gobe zaka mutu .

Inji Imam Hasanul Mujtaba (a.s)
Bihar J 44 Shafi na 139

Muhammad S Tomo ✍🏽

21/06/2026

LABARIN MAI ZAMANI (Ajtf) - 1
Fassarar Hausa

Muhammad S Tomo

21/06/2026

Kada ka cika Idanun ka da kallonsu(Iyaye) face da Rahama da tausasawa ,kada ka daga muryar ka sama da tasu , kada ka Hannun ka sama da tasu , Kuma kada ka taba shigewa Gaban su (A Lamurra).

Inji Imam Sadik (a.s)
Bihar J 71 Shafi na 79

Muhammad S Tomo ✍🏽

Want your business to be the top-listed Media Company in Najaf?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address

No 1
Najaf
3131451