Alfallatee
Your vibe attracts your tribe
let build the bright future together
YA KAMATA GWAMNATI TASA IDO KAN AIKIN ƳAN BANGA
Muna kira ga Gwamnatin Jihar Neja da kuma Gwamnatin Tarayya dasu ƙara sa ido tare da yin cikakken duba kan yadda wasu ƴan banga ke gudanar da ayyukansu domin tabbatar da cewa suna aiki ne bisa doka, adalci, da mutunta haƙƙin ɗan Adam.
A wasu lokuta, ana samun zarge-zargen cewa wasu daga cikin rikice-rikicen da s**a shafi Fulani suna ƙara ta'azzara ne sak**akon yadda wasu ƴan banga ke gudanar da ayyukansu ba tare da bin ƙa'ida ba. Idan har akwai wanda ya aikata laifi, doka ta tanadi yadda za'a bi domin gurfanar dashi gaban hukuma. Bai k**ata a ɗauki laifin wasu kaɗan a ɗora wa al'umma baki ɗaya ba.
Ya k**ata ƴan banga su tuna cewa Fulani ma 'yan Najeriya ne kuma 'yan Adam ne k**ar kowa. Samun ɓata-gari a cikin kowace al'umma baya bada hujjar cin zarafi, k**a, ko kashe waɗanda basu da hannu a wani laifi. Adalci yana nufin a hukunta mai laifi, ba a hukunta mara laifi ba.
Muna kira ga hukumomin tsaro da gwamnati dasu binciki duk wani zargi na take haƙƙin jama'a tare da ɗaukar matakin da ya dace domin kare rayuka, dukiyoyi, da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.
Ku saurari wannan bidiyon abun ya faru ne a kwanakin nan a yankin Ƙaramar Hukumar Rafi.
Allah Maɗaukakin Sarki Ya kawo mana zaman lafiya, haɗin kai, da adalci a Jihar Neja da Najeriya baki ɗaya. Amin.
Episode 2