Matattarai Labarai

Matattarai Labarai

Share

Kamfanin jarida

26/08/2022

RANAR HAUSA TA DUNIYA

Su Waye Hausawa?

Daga Al-mansoor Gusau

Hausa al'umma ce dake zaune a Arewa maso yammacin tarayyar Nijeriya da kuma kudu maso yammacin Jamhuriyyar Nijar.

•Al'umma ce mai ɗimbin yawa, sun bazu a cikin ƙasashen Afirka da ƙasashen Larabawa, kuma a al'umma ce mai matukar hazaƙa, aƙalla akwai sama da mutane miliyan hamsin (50) wadanda harshen Hausa shi ne asalin harshen da su ke magana da shi.

•A tarihi ƙabilar Hausawa na tattare a salasalar birane watau alqarya. Hausawa dai sun sami kafa daularsu ne tun daga shekarun 1300's, sa'adda s**a sami nasarori da dauloli k**ar su daular Mali, Songhai, Borno, da kuma Fulani, a karni na 19 Hausawa suna amfani da Doki ne domin yin sifiri da balaguro.

•Mutane kimanin sama da miliyan 50 ne ke magana da harshen Hausa a Najeriya, Nijar, Arewacin Gana da kuma wasu al’umma daga yankin Kaolack a Senigal har zuwa Khartum dake ƙasar sudan, asalin inda zuciyar Hausawa take shi ne garin Kano, Katsina da Sokoto.

•Asalin al’ummar Hausawa maguzawa ne, amma sun shafe daruruwan shekaru da karbar addinin musulunci ƙarƙashin mulkin sarakunan Haɓe, wanda s**a daina yin bori da tsubbace-tsubbace, zuwan Shehu Usman Ɗan Fodio ne yasa ya kawar da mulkin wadannan sarakunan na ƙasar Hausa, ta hanyar yaƙar Hausawa da sarakunansu na haɓe a Gobir, Zazzau da wasu yankunan ƙasar hausa. Wanda wannan juyin mulkin ne yasa Usman Ɗan Fodio ya kafa Daular Fulani a Hausa Fulani a ƙasar Hausa Kuma Hakan yasa masarautun ƙasar Hausa sun kasance a ƙungiyar Tuta ɗaya na Usman Ɗan Fodio.

•Hausawa suna kiran al’adunsu da al’adan gargajiya, wacce su ke yi duk shekara, ko a talabijin ko Bidiyo, ko kuma aikace cikin al’amuran yau da kullum.

•Na daga cikin rubutun Hausawa, suna yin rubutu ne asali da Ajami, rubutu ne da haruffan larabci amman a luggar hausa, kuma suna rubutawa ne a fallen takarda.

Harshen Hausa yana da ire-ire da yawa k**ar haka:

GABACIN HAUSA.

Kanawa
Kataguwa
Hadejawa
Gumelawa
Katsinawa

YAMMACIN HAUSA.

Daurawa.
Sakkwatawa.
Katsinawa.
Kurfayawa.
Gobirawa.
Adarawa.
Kebbawa.
Zamfarawa.

Babu ko shakka harshen Hausa, rayayyen harshe ne da Allah (SWT) ya daukaka kima da darajarsa a duniya, domin kuwa shi kadai ne harshen da ke iya aron haruffan wani harshe ya yi rubutu da shi da harshensa na Hausa, mai asalin harshen ya kasa karanta abunda Bahaushe ya rubuta da haruffansa.

Ajamin Larabci: - Bahaushe ya ari haruffan Larabci ya mayar da su na Hausa, wanda Balarabe ba zai iya karantawa ba, kuma ya tabbatar da haruffansa ne aka juya.

Ajamin Boko: - Haka zalika Bahaushe ya ari haruffan Boko na Ingilishi ya rubuta magana da harshensa na Hausa Bature ba zai iya karantawa ba, dole sai dai kallo ko kuma ya nemi sani a gurin al’ummar Hausawa.

Al’ummar Hausawa ne ko da Addinin Musulunci ya shigo kasarsu ta Hausa ya tarar da su da kyawawan halaye da dabi’un da su ka yi dai-dai da koyarwar Addinin Musulunci, shi ya sa ma Bahaushe ke yi wa kabilun Nijeriya da su ka karbi Addinin Musulunci kallon hadarin kaji:

MISALI:

•Zumunci.
•Kunya.
•Kara.
•Taimako.
•Kyamar zina.
•Kyamar sata.
•Auren mace fiye da daya.

- Kai rabu da shi Musulunci Bayarrabe.
- Kai ai ka san daga baya ya Musulunta.
- Kai ai ka san asalinsu ba Hausawa ba ne.

Muna rokon Allah (SWT) ya cigaba da daukaka kima da darajar al’ummar Hausawa a Nijeriya, Nijar da duniya baki dayanta, Allah (SWT) ya kawo zaman lafiya, kwanciyar hankali, walwaha, arziki a cikin al’ummar Hausawa da Addinin Musulunci, Allah (SWT) ya zaunar da Arewacin Nijeriya da Kudancin Nijar da daukacin kasashen lafiya alfarmar Annabi Muhammad (SAW).

AL’MANSOOR GUSAU,
ADVOCATE.

26 August 2022.

Photos from Matattarai Labarai's post 07/05/2022

Bashir Ahamad Kenan...........

Wato jama'a shima Bashir Ahamad ya dage sai ya zama dan Majalisar Wakilan Nijeriya mai wakiltar Gaya-Ajingi-Albasu a karkashin jam'iyar APC 2023

Saidai kuma khas Bashir Ahamad ya manta cewa shi mutum ne mai halin dan tsako samu kaki dangi.

Domin Bashir Ahamad ya zama babban mataimaki na musamman ga shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a bangaran sabbin kafufin sada zumunta a 2015 amma har kawo yanzu da nake wannan rubutun Bashir Ahamad bai taimaki yan Social Median jihar kano ba bare muce Nijeriya.

Yau kusan shekaru 7 kenan Bashir Ahamad na aiki da shugaba Buhari a matsayin mataimaki na musamman bangaran sabbin kafufin sada zumunta amma ko sau daya Bashir Ahamad bai taba tunanin ya taimaki masoya kuma magoya bayan shugaba Buhari yan Social Media ba.

Bashir Ahamad Kenan" Yanzu a haka kake tunanin zama dan Majalisar Wakilan Nijeriya? bayan baka da kyakkyawar mu'amala da mutane.

Yanzu haka Bashir Ahamad baida kyakkyawar halaka da yan Social Median Gaya-Ajingi-Albasu didda kasancewar shi hadimin shugaba Buhari bangaran Social Media wanda hakan ya tilasta mai tallata kanshi da kanshi a cikin kafafen sada zumunta.

Saboda haka nake bama al'ummar kana nan hukumomin Gaya-Ajingi-Albasu shawarar cewa su waye kafun a masu kanta waye domin na tabbata cewa Bashir Ahamad kanta waye yake shirin masu 2023.

Daga Abubakar A Adam Babankyauta.

21/03/2022

Indai Gudun Hawala Kake Daga Yau Ta Kare, Yan Ta'addan Daji Sun Fadawa Wani Magajin Gari Kafun Su Kashe Shi

Daga Abubakar A Adam Babankyauta

Wato jama'a yan bindigan daji masu hallaka jama'a sun kashe hakimi sannan s**a tayar da garin shi baki daya a cikin jihar Zamfara.

Majiyar mu ta labarta mana cewa yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 25 da s**a haɗa da Hakimi da wasu sarakunan gargajiya a ƙaramar hukumar Bukkuyyum a jihar Zamfara.

Yan bindigar sun abka ƙauyen Ganar Kiyawa ne a ranar Lahadi s**a kashe mutanen, k**ar yadda mazauna yankin s**a shaida wa majiyar mu.

Mutanen garin sun ce yan bindigar sun shiga garin na Ganar Kiyawa ne saman babura, kuma bayan mutane sun tsorata sun fara tserewa, yan bindiga s**a dinga harbinsu, cikin waɗanda aka kashe har da hakimin garin Bala Muhammadu da Magajin gari Sani Salihu da wani bafade da ake kira Sharu.

Wani wanda labarin ya rutsa da sh8 yace da ni da Hakimi da Magajin Gari mun yi gudun kilomita uku, kuma da s**a cimma Magajin Gari s**a tambaye shi me yake wa gudu ya ce wahala, sai s**a ce to ta ƙare, s**a harbe shi," a cewar wani mazauni garin da yake bayar da labarin da ƴar magajin garin da aka kashe ta faɗa masu bayan sun tsira.

Ya ce sun samu gawar mutum 25 da maharan s**a kashe, kuma ana ci gaba da binciken wasu gawawakin a daji."

Ya ce an yi wa gawar mamatan Sallar jana'iza ne a garin Adabka. Ya ce adadin na iya ƙaruwa saboda har yanzu akwai mutanen da ba a gani ba.

Maharan sun tarwatsa garin Ganar Kiyawa inda dubban mutane s**a tsere zuwa wasu ƙauyuka makwabta.

Hakimin Adabka ya shaidawa BBC cewa mutanen da ke cikin garinsa sun kai kusan mutum 3,000.

A cikin wata sanarwa bayan kai harin, gwamnatin jihar Zamfara ta jajantawa mutanen garin tare da bayar da umarnin kai masu tallafi.

Muna rokon ubangiji Allah ya nuna mana karshen wannan lamarin tare da azurta kasar mu Nijeriya da zaman lafiya mai daurewa.

Want your business to be the top-listed Media Company in Asokoro?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address

Zone 1 Wuse Abuja
Asokoro
08030471966