Da'irar Azare

Da'irar Azare

Share

An Bude Wannan Shafi Ne Domin Isar Da Sakonnin Harka Islamiyyah Na Musamman Na Da'irar Azare Dama Kasa Baki Daya.

13/05/2022

"Wannan yakarmu ake yi amma kuma duk ana ta baganniya. Yanzu mutane sun zama babu wanda zai yi magana a saurare shi, sai an ce shi wane ne, sai a duba kai wane ne, kai dan mene ne kai. Ta haka suke kallo. Wannan abu da ban al’ajabi. Dama yana cikin yakin da s**a kawo mana, sai da s**a kawo yakin rarraba kawukan mutane sannan s**a shigo da wani nau’in yakin, sai ya zama kowa yanzu ya yi magana sai ka ga shi daban-daban ne kawai.

"Idanun mutane ya rufe. Su ba su karbar gaskiya idan sun ji ta sai daga wurin wane s**a ji. Kuma ba gaskiya kadai, idan Malam wane Malaminsu ne komai ya fada ya yi daidai. Gaskiya ya yi, ko ba daidai bane, daidai ne. Idan ko wancan Malam ba Malaminsu bane, to komai ya fada ba daidai bane. Haka ake yi? Ita gaskiya sunanta gaskiya, inda ka ganta sai ka ce haka take. Amma inaa. Yanzu an shamakancin mutane an sa musu irin wannan tunanin kai kawai kowa da kungiyarsa. Kowa da kungiyarsa, wannan kungiyanci ya shigi mutane, ya zama shi ne ya zama ginshiki ya hana su gane komai".

*-Shaikh Ibraheem Zakzaky a yayin ganawarsa da wakilan bangarorin Harka Islamiyya a ranar Juma'a 6 ga watan Shawwal 1443 daidai da 6 ga watan Mayun 2022 a gidansa dake Abuja.*

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Azare?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address

Matsango
Azare
07046431819