BILAL BN RABAH RADIO
Shashine domin labaru da al'amuran yau da kullum na gidan radio BILAL BN RABAH ONLINE .
08/05/2023
** BILAL BN RABAH ONLINE RADIO**
** SHIRIN LABARUN MAKO**
Yau LAHADI: 07/05/2023M, Wanda yayi dai dai da 17/10/1444H.
** DAFARKO MUHIMMAN KANUNSU**
(1) Makarantar Bilal BN RABAH, ta dawo domin cigaba da gudanar da karatu a makarantar bayan shape kwanaki suna hutu.
(2) Hukumar gudanarwan makarantar Bilal bn Rabah ta Mika sakon taya murna wa daya daga cikin malaman makarantar bisa samun sarauta da yayi.
(3) Hukumar makarantar Bilal bn Rabah taja hankalin dalibai tare da yi musu gargadi akan zuwa da ababen da s**a haramta a makarantar. tare da hukunda Wanda Basu dawo makarantar ba a satin da akadawo.
(4) Hukumar gudanarwan makarantar Bilal bn Rabah, ta haramta wa daliban makarantar soyayyar a tsakanin 'yan uwansu dalibai, musanman a makarantar.
YANZU KAN MAI SAURARO SAI KA GYARA ZAMA DOMIN JIN CIKAKKAN SU WANDA NI SALISU ABUBAKAR DANDIJA ZAN KARANTU.
(1) A jiya Asabar ne makarantar Bilal bn Rabah,ta dawo domin cigaba da gudanar da karatu a makarantar, biyo bayan shape kwanaki suna hutu a qalla na kwanaki hamsin da daya(51) suna hutu,da yake sannar da sakon dawowan makarantar, shugaban makarantar Bilal bn Rabah malam Abdurrahman Yusuf Adam sai yafara da Mika godiyarsa wa Allahu subuhanahu wata'ala daya bamu ikon dawowa daga hutu lpia,sai ya Kara da cewa makarantar zata cigaba da gudanar da karatu kamar yadda da saba,tare da daukan tsattsauran mataki,akan duk Wanda ya Saba dokan makarantar.daga karshe sai ya shawarci daliban da su cigaba da Mai da hankali akan karatunsu.
(2) Hukumar gudanarwan makarantar Bilal bn Rabah,ta Mika sakon taya murna wa daya daga cikin malaman makarantar Mai suna ( malam Usman Jibril Umar) bisa samun sarauta da yayi a lokacin gudanar da hidimar sallah, Wanda Allah ya zabenshi a matsayin( SA'IN JARMAI NA FARKO) dake karamar Hukumar kanam a jihar plateau (jos) wannan matsayin da yasamu yazune bisa irin gudumawa dake bayarwa a yankinsa.shima a nashe jawabin Mai girma SA'IN JARMAI NA FARKO malam Usman Jibril Umar sai ya nuna farin cikinsa wa daukacin al'ummah musulmai da s**a taya Shi farin, daga karshe sai yayi godiya wa Hukumar gudanarwan makarantar Bilal bn Rabah, bisa nuna masa soyayya akan haka.
*** MAI SAURARO KAR DAI KASHA'AFA KANA SAURARON SHIRIN LABARUN MAKO NE DAKE ZUWA MAKA DAGA NAN SHASHIN LABARU DA AL'AMURAN YAU DA KULLUM NA GIDAN RADIO BILAL BN RABAH.***
**TO MADALLAH BARKANMU DA RATSE*
(3) Hukumar gudanarwan makarantar Bilal bn Rabah, ta ja hankalin dalibai tare da yi musu gargadi akan zuwa da ababen da s**a haramta a makarantar,tare da hukunta wanda Basu dawo a satin da akadawo ba, wannan batun yafitone a lokacin da a ke gudanar da taron dalibai na mako wato (Assembly) Wanda makarantar tasaba yinsa a dukkan farko mako domin tunatar da dalibai muhimman batuttowa dake faruwa a makarantar, da yake gudanar da Assembly malam zayyad Hussain sai ya gargadi daliban dasu zamo masu bin dokokin makarantar sau da kafa.daga karshe sai ya karantu wani Shashi daga cikin dokokin makarantar,Wanda shashin na sha biyar (Sections 15 ) shashin da ya haramta wa dalibai zuwa da wayan ( hand set) da dai sauransu.
har illah yau Hukumar makarantan Tasha alwashen hukunta daliban da Basu dawo makarantar ba akan lokacin da zaran sun dawo makarantar zata hukunta su.
(4) Hukumar gudanarwan makarantar Bilal bn Rabah, ta haramta wa daliban makarantar soyayya a tsakanin'yan uwansu dalibai, wannan haramcin ya zune a lokacin da mahukunta makarantar takai wani sumame yadda tasamu dalibai suna soyayya a tsakanin su,da yake shaidawa wa manema labarai akan matakin da makarantar ta daukan akan masu soyayya a makarantar a offishin sa, shugaban makarantar sai tabbatar mana da cewa makarantar zata sallamisu sannar Kuma gayyatan iyayen Baki.
wani 6angaren kuma Hukumar gudanarwan makarantar Bilal bn Rabah tana sanar da daukacin al'ummah da masu sha'awar Shiga ( DAURA ) Wanda tasaba gudanarwan duk shekara a tsakanin Yara domin ya Basu damar iyya hada baki, a wannan shekaran ma takawo waasu sha'awar Shiga, dasu garzawo haraban makarantar Bilal BN RABAH.
DAMA WANNAN REPORTAN MUKE KAWO KARSHE LABARUN MAKO, NA WANNAN MAKON SAI WANI MAKO IDAN ALLAH YAKAIMU ZAKUJI MU DA WASU.
YANZU KAN AMADADIN DAUKACIN GUDANARWAN MAKARANTAR BILAL BN RABAH DAKE DAUKAN NAUYIN KAWO MUKU.
SAI EDITOR MU NA WANNAN MAKON
ZAYYAD HUSSAIN
SAI NI DANA SHIRYA KUMA NA GABATAR
SALISU ABUBAKAR DANDIJA.
12/04/2023
**BILAL BN RABAH ONLINE RADIO**
** SHIRIN LABARUN MAKO**
Yau LARABA: 21/9/1444AH.
Wanda yayi dai dai da 12/04/2023M.
**DAFARKO MUHIMMAN KANUNSU**
(1) Hukumar gudanarwan makarantar Bilal bn Rabah ta bada hutun sallah na tsawon kimanin kwanaki Ashirin da shida(26) daga Ranar 09/04/2023 zuwa Ranar 06/05/2023.
(2) sannar Kuma Hukumar makarantar Bilal bn Rabah tana Kara tunatar da daukacin iyayen Yara akan suna biyan kudin makarantar 'yayan su akan lokacin,da zaran an Shiga wani sabon zangon karatu.
(3) shugaban makarantar Bilal bn Rabah ya tunatar da dalibai akan su Kara dagewa wajen cigaba da yin Addu'o'i wa kasa dama jihar Bauchi na samun dawwamammen zaman lpia.
(4) Hukumar gudanarwan makarantar Bilal bn Rabah ta ja hankalin daliban makarantar da suyi koyi da abinda suke karantawa na alqur'ani.
** YANZUKAN MAI SAURARO SAI KA GYARA ZAMA DOMIN JIN CIKAKKAN SU WANDA NI SALISU ABUBAKAR DANDIJA ZAN KARANTU.
(1) Hukumar gudanarwan makarantar Bilal bn Rabah ta bada hutun sallah har na tsawon kimanin kwanaki Ashirin da shida (26) daga Ranar 09/ 04/2023 har izuwa ranar 06/04/2023, sakon hutun sallah yafitone daga bakin shugaban makarantar Bilal bn Rabah, malam Abdurrahman Yusuf Adam yace sakon hutun ya biyo bayan shape kwanaki suna gudanar da karatu a cikin wannan watan Ramadan kamar yadda makarantar tasaba gudanarwan.
sai shugaban makarantar ya cigaba da Mika godiyar sa wa Allah da ya kawo mu yau muna cikin watan Ramadan mai alfarma da kuma daraja.daga karshe sai yayi Addu'ar da fatan kuwa sai hidimar sallah lpia.
(2) Shugaban makarantar Bilal bn Rabah malam Abdurrahman Yusuf Adam, Yana Kara tunatar da daukacin iyayen Yara akan suna biyan kudin makarantar'yayan su akan lokacin, da zaran an Shiga sabon zangon karatu, domin bayar wa makarantar tsare-tsarenta akan lokacin batare da wani matsalolin a cikin karatun 'yayan su ba,ya sannar da wannan sakonne a lokacin da yake isar da hutu a harabar makarantar, daga karshe sai ya roki Allah, sannar Kuma da daukacin iyayen Yara akan haka.
** MAI SAURARO KAI DAI KASHA'AFA KANA SAURARON SHIRIN LABARUN MAKO NE DAKE ZUWA MAKA DAGA NAN SHASHIN LABARU DA AL'AMURAN YAU DA KULLUM NA GIDAN RADIO BILAL BN RABAH.**
** TO MADALLAH BARKANMU DA RATSE**
(3) Shugaban makarantar Bilal bn Rabah"Malam Abdurrahman Yusuf Adam"ya tunatar da daliban makarantar akan su Kara dagewa wajen cigaba da yin Addu'o'i wa kasa dama jihar Bauchi na samun dawwamammen zaman lpia, wannan tunatarwan yafitone a lokacin da yake ganawa da manema labarai a cikin makarantar Bilal bn Rabah, Abdurrahman Yusuf Adam sai yafara da nuna muhimmanci Addu'o'i wa kasa dama jihar baki daya, idan akayi la'akari da yanda muke cikin wani hali a kasan.daga karshe sai yayi Addu'ar Allah yakawomana sauki a cikin rayuwanki.
(4) Hukumar gudanarwan makarantar Bilal bn Rabah ta ja hankalin daliban makarantar dasu yi koyi da abinda suke karantawa na alqur'ani da Hadisai na manzon Allah sallalla'hu Alaihi wasallam, domin su dace da alkhairi da yake cikin sa, da yake wannan Jan hankalin wa daliban makarantar ("" malam MUHAMMAD MUHAMMAD AS GUNNAH) sai ya fara da nuna musu muhimmanci aikin da abinda mutum yakoya domin bashi kariya daga karshe Muhammad Muhammad sai yayi Addu'ar Allah yasanya alkhairi a cikin wannan watan Ramadan da muke cikin sa.
wani 6angari kuma Hukumar gudanarwan makarantar Bilal bn Rabah ta yi nasiha wa daliban makarantar da suji tsoron Allah a lokacin da suke gudanar da hidimar karamar sallah,kamar shigar da bata dace da addini kamar( MATA) ko zuwa party da sauransu kamar (MATA ko MAZA), Daga karshe Hukumar gudanarwan makarantar sai tayi Kira wa iyayen Yara akan su Riki kiwon da Allah yabasu domin Abin tambayane a gobe kiyama.
**DAMA WANNAN REPORTAN MUKE KAWO KARSHE LABARUN MAKO SAI WANI MAKO IDAN ALLAH YAKAIMU ZAKUJI MU DA WASU***
YANZU KAN AMADADIN DAUKACIN GUDANARWAN MAKARANTAR BILAL BN RABAH,TA DAUKI NAUYIN KAWO MUKU.
SAI WANDA YA TACE MANA SHI KAMAR YADDA KU KAJI, MUHAMMAD ZAYYAD HUSSAIN.
SAI NI DANA SHIRYA KUMA GABATAR.
SALISU ABUBAKAR DANDIJA.
SAI WANI MAKO
10/04/2023
05/02/2023
**MOCK EXAMINATION 2022/2023 ACADEMIC SESSION***
Hukumar gudanarwan makarantar Bilal BN RABAH ta shirya wa daliban makarantar jarrabawa gwaji na (mock examination) a tsakanin daliban domin tantance masu kokari a tsanin daliban kamar yaddan ta saba a kowace shekara.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Website
Address
Bauchi