ANNUR RADIO FM

ANNUR RADIO FM

Share

Broadcasting for development

15/11/2025

An fasa auren Boniface saboda ya ari salo irin na Hakimi! 😳

Budurwar Victor Boniface ta soke shirin auren su saboda gano wani babban dalili, wanda zai sa ba zata ci dukiyar ɗan wasan ba ko da ƙaddara tasa sun rabu a gaba.

Ɗan wasan na Najeriya, ya shirya aure da Bajamar Rikke Ermin ƴar ƙasar Norway, amma bikin ya rushe saboda ta gano wani sirri da yake ɓoye mata.

Ermin ta dage a ɗaura musu aure kan yarjejeniyar raba dukiya, wanda hakan ke nufin idan sun rabu, za a raba gaba ɗaya dukiyar Boniface biyu a bata rabi.

Boniface bai musa mata a kan hakan ba, inda ya amince kuma ya sanya hannu a kan za a raba dukiyar sa biyu a bata rabi idan ƙaddara ta sa sun rabu anan gaba, domin a zahiri babu komai dake ƙarƙashin sunan sa cikin dukiyar sa.
Boniface ya yi Rijistar komai na dukiyar sa ne da sunan mahaifiyar sa. 😃👌🏻

Bayan Ermin ta gano haka, sai ta janye auren sa, inda ta fasa bikin, kuma ta kawo ƙarshen soyayyar su ta tsawon shekaru 4.

Dole ne Hakimi ya yi alfahari da wannan babban Sojan na sa 👏🏻😂

• Fagen Wasanni

Photos from ANNUR RADIO FM's post 21/10/2025

BREAKING NEWS:
Yesterday at the Presidential Villa, I met with a PLAN International delegation led by its Director of Programme, Quality and Innovation, Helen Mfonobong Idiong.

During the visit, I also invited a teenager, Joy Ogah, to take over my seat as the Vice President for a day and address the nation.

In my remarks, I assured stakeholders and development partners of President Bola Ahmed Tinubu’s commitment to promoting girl-child education across Nigeria.

We will continue our engagement with PLAN International and explore how the force and strength of government can be brought to bear on your solid advice regarding girl-child education.

21/10/2025

ANA WATA GA WATA,
Da ɗumi ɗumi: Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Gano Almundahanan Kuɗaɗe A Hukumar BAROTA

Gwamnatin Jihar Bauchi ta dauki matakin tsabtace ayyukan hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar, BAROTA, bayan zarge-zargen wawurar kudade da kuma rashin ingantaccen gudanarwa da s**a durkusar da ayyukan hukumar a ‘yan watannin baya bayan nan.

Domin magance matsalar, gwamnatin ta nada kwararre a fannin kula da zirga-zirga, Abdulmumini Aliyu, a matsayin mai ba da shawara wanda zai jagoranci sabunta ayyukan hukumar tare da dawo da amincewar jama’a akanta.

Aliyu, wanda shi ne Manajan Darakta kuma Shugaba na kamfanin Girdo Technical and Engineering Services Limited, ya bayyana cewa binciken farko da aka yi ya gano shaidun aikata cin hanci da rashawa, karkatar da kudade da kuma rashin kyakkyawan tsarin gudanarwa daga tsohuwar shugabancin hukumar ta BAROTA.

Ya ce wannan mummunan yanayi ya haifar da raunin kwarin gwiwar ma’aikata da kuma tsaikon biyan albashi, wanda ya haddasa durkushewar ayyukan hukumar a fannonin kula da zirga-zirga da kiyaye doka a kan tituna.

Aliyu ya tabbatar da cewa yana da niyyar sake gina hukumar bisa ginshikin gaskiya da rikon amana, tare da mayar da hankali kan dawo da kwanciyar hankali da daidaito a tsakanin ma’aikata.

Ya kuma roki jami’an hukumar da s**a bar aiki saboda rikicin kudi da rashin shugabanci su koma bakin aiki, inda ya tabbatar musu cewa sabon tsarin gudanarwar zai magance korafe-korafensu.

Want your business to be the top-listed Media Company in Bauchi?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Address

Nassarawa Jahun, Unguwar Dim, Behind Bilal Bn Rabah Mosque
Bauchi