M A Foundation
Wannan page an bude shine domin watsa labarai da al'amuran yau da kullum. We opened this page for daily news
11/05/2026
Magana ake ta wanda zai iya kuma wanda zaici zabe cikin ruwan sanyi da izzinin Allah
Ya yan uwa na al'ummar Jihar masu girma da Daraja, Lokaci ya yi da za mu zabi shugaba mai ilimi, adalci, da kishin talaka. Muna gabatar muku da ɗan takarar mu Wanda ba boyayye bane ga kowa, mutum mai nagarta kuma ƙwararren lauya wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare haƙƙin jama’a da tabbatar da gaskiya.
Me yasa ya dace ku zaɓe shi? Lauya ne mai cikakken sanin doka da tsarin shugabanci, Mutum ne mai gaskiya da riƙon Amana, Wanda ya fahimci matsalolin talaka kuma yake da niyyar kawo mafita, yana da ƙwarewar sasanta rikici da haɗa kan al’umma.
Ina da tabbaci Kamar yadda kuka sani Mak**a Babba ne in samu ticket zamu rungumi kowa a matsayin uwan mu daya uban daya, ba gaba ko nununa wariya, kuma shine zai yi shugabanci bisa adalci, gaskiya, da kawo cigaba wa jama’a
Ga sauran al'ummar Jihar Bauchi kuwa, Kamar yanda na jima ina fada muku hakika yanzu ba lokacin gwaji bane, lokaci ne na zaɓar mutum mai ilimi da hangen Nesa, mu haɗa kai mu bai wa ƙwararren lauya dama domin samar da ingantaccen shugabanci, cigaba mai ɗorewa, da makoma mai kyau ga al’ummarmu.
Mu sani adalci da gaskiya, da da kawo cigaba wannan shine aniyar mu Kuma itace alkawarinmu ga al'ummar Jihar Bauchi masu albarka, ina kira ga dukkan illahirin al'ummar Jihar da membobin mu na APC ku fito mu mara masa baya domin nasarar Jam’iyyar mu ta APC, da kuma cigaban mu gaba ɗaya.
I Stand With Mak**a Babba🥰🥰🥰✌️
14/07/2025
A rasuwar shugaba Muhammadu Buhari an samu rabuwar kai, da masu masa addu'ar alheri dana tsiya, amma lokacin rasuwar Umar Musa Yar'adua dukkan ƴan Nigeria sun haɗa kai wurin faɗawa alhini tareda yi masa addu’a, wanda har ya zuwa yau ɗinnan in ranar mutuwar Yar'adua ta zagayo sai Kaga ana tunawa dashi ta ko'ina a faɗin ƙasar nan. Mai yasa haka ne, dukda kasancewar Buhari, shugaba mafi kwarjini da mukayi a cikin Shawagabannin Nigeria???
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Bauchi