Labaran Duniya - News
Wanna page ne da zai rika kawo maku labarai da abubuwan yau da kullum
25/02/2026
Wasu ’yan majalisar dokokin ƙasar Amurka ƙarƙashin jagorancin ɗan majalisa Riley Moore sun miƙa wa Fadar White House rahoto na musamman kan halin da ake ciki a Najeriya, musamman dangane da zargin tauye ’yancin kiristoci.
Rahoton ya buƙaci gwamnatin Amurka ta sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargi da take hakkin addini, tare da kakaba takunkumi kan duk wanda aka samu da hannu wajen cin zarafin mabiya addinai, ciki har da hana su biza.
’Yan majalisar sun kuma nemi a duba yiwuwar dakatar da shigo da wasu kayayyaki daga Najeriya, ciki har da naman shanu, domin matsa lamba ga masu tayar da hankali su ajiye makamansu.
Haka kuma, tawagar ta ba da shawarar cewa Najeriya ta daina sayen makamai daga Rasha, maimakon haka ta koma sayen makaman Amurka a matsayin wani ɓangare na ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.
Bugu da ƙari, rahoton ya buƙaci gwamnatin Najeriya ta soke wasu dokoki da s**a haɗa da na shari’a da na ɓatanci, waɗanda a cewarsu ana amfani da su wajen gallaza wa wasu mabiya addini.
01/02/2026
China ta Kafa Tarihi Bayan kammala Wani babban aiki na hanyoyin sufuri a ƙarƙashin Ruwa
30/01/2026
Mataimaki na musamman ga gwamnan Umaru Radda kan kafafen watsa labaru MS Ingawa a wata sanarwa da ya fitar, ya ce tuni aka saka hannu a kan yarjejeniyar gina gidajen da wani kamfani ,mai suna COSMOS Residential City Nigeria Limited.
Click here to claim your Sponsored Listing.