Iambello143
By the grace of God we must become the change we wish to see in the world. I love you all my people's
14/02/2026
Mahaifi zai iya dawowa gida da gajiya mai nauyi.
Amma yana shigowa, zai ajiye gajiyar gefe guda, ya dauki yaransa yana wasa da su kamar ba shi ne ya sha wahalar rana ba.
Alhali takalminsa ya tsage.
Rigarsa daya ce take yawo a jikinsa.
Zuciyarsa tana cike da lissafin yadda zai biya kudin makaranta, kudin abinci, da maganin mahaifiyarsu.
Amma duk da haka, zaka ga yana fada musu cewa:
"Kada ku damu, komai akwai shi, kuma komai zai yi kyau inshaAllah."
Zai iya jure yunwa domin su koshi.
Zai iya jure sanyi domin su ji dumi.
Zai iya jure wulakancin kowa a waje, amma idan ya dawo gida, zai tsaya a matsayin "Sarki" kuma garkuwar da kowa yake alfahari da ita.
Wannan sam ba wasa ba ne...
Wannan shi ake kira mahaifi.
Shi ne mutumin da yake gina rayuwar wasu, alhali tasa tana rugujewa. Shi ne jarumin da ba ya bukatar lambar yabo, sai dai ganin yaransa sun zama mutane.
Allah Ya albarkaci mahaifanmu, wadanda suke raye Allah Ya kara musu lafiya da nisan kwana, wadanda s**a rigamu gidan gaskiya Allah Ya kyautata makwancinsu. 🤲
Wace kalma daya zaka iya cewa game da Mahaifinka? 👇
Iambello143
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Delta State