Darul Hadeeth Wal-Fiqhu
Anbude Wannan Shafi ne Domin Samun Karatukan Maluman Sunnah Daban-Daban A Fadin Afirka.
29/10/2025
Jiya na ji wani kasurgumin makaryaci Dan Bidi'a yana yi wa Ahlus-Sunnah sharri, yana cewa ba su taɓa yin wata lacca mai taken “Son Annabi Muhammad ﷺ” ba.
Wannan ƙarya tasa ta tunatar da ni karatun littafin Ash-Shifā, wanda Sheikh Abdurrazaq Haifan (hafizahullah) yake karantawa. A cikin darussa na 002 da 003, Malamin ya gabatar da karatun mai taken “Ayoyin Ɗaukakar Annabi ﷺ.”
Ina roƙon duk mai son gaskiya da neman ilimi da ya samu lokaci ya saurari waɗannan darussa guda biyu (tsawon sa’o’i biyu kacal). Zai ga yadda Malamin ya yi bayani mai zurfi, cike da ƙauna, ladabi da girmamawa ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.
Lallai, waɗannan karatun suna ƙara haske ga zuciya, suna kuma ƙarfafa soyayya da biyayya ga Annabi ﷺ, wanda shi ne ginshiƙin addininmu.
23/06/2025
Mutane da dama a ƙasashen Faransa, Girka, Pakistan da dai sauran su sun fito domin yin alla-wadai da harin da Amurka ta kai kan Iran a wani ɓangare na rikicin Isra'ila da Iran.
A birnin Washington DC, ɗaruruwan mutane sun je gaban fadar shugaban Amurka domin nuna rashin amincewarsu da matakin na Trump.
Trump dai ya ce "ya kai harin ne kan cibiyoyin sarrafa makamashin nukiliya na Iran domin daƙile yunƙurin ƙasar na mallakar makamin nukiliya".
~BBC HAUSA.
Alamar son Annabi S.A.W
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the practice
Telephone
Website
Address
Funtua
KT-NG