Gombe Reporters
Sahihan Labaru Da Dumi Duminsu
06/07/2026
Rikicin Manoma da Makiyaya a Daban Fulani, Jihar Gombe
Mazauna garin Daban Fulani da ke Ƙaramar Hukumar Kwami a Jihar Gombe sun yi kira ga gwamnati da jami'an tsaro da su gaggauta ɗaukar mataki kan yawaitar rikicin manoma da makiyaya a yankin.
Wasu daga cikin waɗanda s**a jikkata sun ce shanun makiyaya sun lalata amfanin gonakinsu da kayan noma na miliyoyin naira. Sun kuma zargi cewa an kai musu hari yayin da suke ƙoƙarin hana dabbobin shiga gonakinsu.
Sun buƙaci a hukunta masu hannu a rikicin tare da ɗaukar matakan tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al'umma. A lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu jin ta bakin makiyayan kan zarge-zargen ba.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Address
Gombe