Ibrahimfky

Ibrahimfky

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Ibrahimfky, Gombe.

13/04/2026

MU’AMALA TSAKANIN HIMLU ARIES (1) DA LIBRA MIZANU (7)

(ba aure kaɗai ba, har abota, kasuwanci da dukkan hulɗar rayuwa)

ASALI DA HALITTA
ARIES HIMLU
Burujin wuta ne.
Mai ƙarfi, jarumta, gaggawa, son jagoranci da ɗaukar mataki kai tsaye.
Yana son nasara, gasa da bayyana abin da ke zuciya.
Ba ya son jinkiri ko shakka.

LIBRA MIZANU
Burujin iska ne.
Mai son daidaito, adalci, sulhu da kyakkyawar mu’amala.
Yana son tattaunawa, zaman lafiya da auna al’amura kafin hukunci.
Ba ya son rikici ko tsauri.

Wuta da Iska
Iska tana hura wuta.
Wuta tana ba iska kuzari.
Saboda haka akwai jan hankali mai ƙarfi a tsakaninsu.
Wannan haɗin yana cikin haɗin da ake yawan gani a ilimin taurari domin suna gaba da juna a da’irar burujai.
Gaba-da-juna yana nufin jan hankali, amma kuma gwaji.

YANAYIN MU’AMALA
SOYAYYA
Akwai jan hankali mai sauri.
Aries yana burge Libra da ƙarfin hali da tabbaci.
Libra yana burge Aries da ladabi da salo.
Matsala
Aries yana son abu nan take.
Libra yana son tunani kafin yanke hukunci.
Aries yana iya zama mai zafi.
Libra yana iya guje wa rikici.
Wannan na iya haifar da soyayya mai ƙarfi amma mai yawan saɓani.

IDAN SUKAI AURE
Aure na iya yin nasara idan an fahimci bambanci.
Aries yana jagoranci da kuzari.
Libra yana kawo daidaito da sulhu.
Idan Aries ya yi tsauri, Libra zai ji an tauye shi.
Idan Libra ya yi jinkiri ko shakka da yawa, Aries zai fusata.
Idan kowa ya koyi abin da ɗan uwansa ya rasa, aure zai yi ƙarfi.

A ABOTA
Abota mai kuzari ce.
Aries yana motsa Libra.
Libra yana kwantar da Aries.
Za su iya taimaka wa juna sosai.
A KASUWANCI DA AIKI
Haɗin yana da kyau idan an raba aiki.
Aries ya dace da fara abu da ɗaukar haɗari.
Libra ya dace da ciniki, sulhu da hulɗa da mutane.

Rikici kan shugabanci na iya tasowa idan ba a fayyace rawuna ba.
DARASI NA RAYUWA
Aries yana koyon haƙuri, sauraro da adalci.
Libra yana koyon ƙarfi, yanke hukunci da ɗaukar mataki.

GASKIYA A HIKIMA
Wannan haɗin mai ƙarfi ne kuma mai muhimmiyar darasi.
Ba mafi sauƙi ba ne, amma yana iya zama mai girma idan an fahimci juna.
Jan hankali yana da yawa, haka nan gwaji.

A ƘASASHE
Taurari alamu ne kawai na halaye da yanayi.
Ba su da ikon tilasta soyayya, aure ko rabuwa.
Allah Shi kaɗai ne Mai iko da zukata da kaddara.
Abin da Ya so ne kaɗai yake tabbata.
Wallahu ta’ala a’alam.

Ibrahim fky al falaky ✍️ 07033105536

13/04/2026

HISAB
A CIKIN SUNA AKWAI SIRRIN DA BA A FIYE LURA DA SHI BA

Mutane da yawa suna jin suna tamkar kira ne kawai.
Ana kiran mutum da shi, ana saninsa da shi,
kawai magana ta ƙare.
Amma masu zurfin nazari sun san cewa suna yana ɗauke da ma’ana fiye da yadda ake zato. Domin harafi yana da nauyi, adadi kuma yana da ishara.
Idan aka tattara lissafin suna sannan aka rage shi da tsarin da 9-9 har sai ya tsaya a lamba guda, ana samun asalin number ɗin da ke wakiltar wani ɓangare na tasirin sunan.

A yau za mu taɓo Number 1 kaɗai.
MA’ANAR NUMBER 1
Number 1 alama ce ta farko, jagoranci, fara abu, dogaro da kai, da son kasancewa gaba.

Mai wannan tasiri a suna yana da wani irin ƙarfi na son ya tsaya da kansa. Ba ya son a rinƙa jan sa a baya. Yakan fi jin daɗin yin abu ta hanyarsa fiye da bin sawun mutane kawai.
Sau da yawa irin wannan mutum yana da burin zama abin koyi ko wanda ake dubawa idan al’amari ya taso.

HALAYENSA
Mai number 1 a suna yakan kasance:
Mai son cin gashin kai
Mai ƙwarin guiwa
Mai saurin yanke shawara
Mai son a gane ƙimarsa
Mai son fara abu kafin kowa
Mai neman cigaba
Idan aka ba shi dama, zai iya zama jagora mai amfani ga mutane da yawa.

ABIN DA YAKE IYA JAWO MASA ƘALUBALE
Kowane ƙarfi yana da inda yake iya wuce gona da iri Haka ma number 1.

Idan ba a daidaita hali ba, yana iya jawo:
Taurin kai
Son a bi ra’ayinsa kawai
Rashin haƙuri
Fushi idan an raina shi
Jin ba ya buƙatar kowa
Saboda haka hikima ita ce a haɗa jagoranci da tawali’u.

ABIN DA YA KAMATA MAI WANNAN TASIRI YA YI
Idan ka ga alamar wannan number ta rage a sunanka, ka yi ƙoƙari
Ka yi amfani da jagoranci wajen taimako
Ka rage girman kai
Ka saurari shawarar wasu
Ka zama mai haƙuri
Ka fara abu mai amfani, ba gardama ba

SAKO NA ƘARSHE
Ba number ce kaɗai ke gina rayuwar mutum ba. Amma wani lokaci tana zama kamar madubi da ke nuna inda ƙarfi yake da inda gyara yake.

Idan ka san inda kafi ƙarfi, to kai amfani da shi da hikima. Idan ka san inda rauni yake, ka gyara shi da natsuwa.
Domin sanin kai shi ne farkon gyaran rayuwa.

ibrahim fky al falaky ✍️ 07033105536

12/04/2026

MU’AMALA TSAKANIN TA**US (SAURU2) DA SCORPIO (AƘRABU8)
(ba aure kaɗai ba, har abota, kasuwanci da dukkan hulɗar rayuwa)

ASALI DA HALITTA
TA**US
Burujin ƙasa ne.
Mai natsuwa, haƙuri, dagewa, son tabbaci da kwanciyar hankali.
Yana son dukiya, aminci da abin da zai dore.
Ba ya son canji ko ruɗani.

SCORPIO
Burujin ruwa ne.
Mai zurfin zuciya, tsananin sha’awa, kishi, sirri da son mallaka.
Yana son gaskiya tsantsa da cikakken aminci.
Ba ya wasa da al’amuran zuciya.

Ƙasa da Ruwa
Ruwa yana ba ƙasa rai.
Ƙasa tana ba ruwa mafaka.
Amma idan ruwa ya yi yawa, ƙasa ta rikice.
Idan ƙasa ta yi tsauri, ruwa ya tsaya.
Wannan haɗin yana da ƙarfi sosai.

YANAYIN MU’AMALA
SOYAYYA
Akwai jan hankali mai tsanani tun farko.
Ta**us yana jan Scorpio da natsuwa da tabbaci.
Scorpio yana jan Ta**us da zurfin soyayya da sha’awa.

Matsala
Ta**us yana son zaman lafiya.
Scorpio yana son zurfi da cikakken iko.
Ta**us yana iya ɓoye taurin kai.
Scorpio yana iya nuna kishi da zargi.
Soyayya mai ƙarfi ce, amma ba mai sauƙi ba.

IDAN SUKAI AURE
Wannan haɗin na iya zama mai dorewa sosai.
Dukansu suna son aminci da riƙon alaƙa.
Ba sa son cin amanar juna.
Amma idan rikici ya shiga
Ta**us ba ya sassautawa.
Scorpio ba ya mantawa.
Idan an gina aure kan gaskiya da tsoron Allah, yana iya zama mai ƙarfi ƙwarai.

A ABOTA
Abota mai zurfi ce amma ba mai sauƙin budewa ba.
Da zarar an amince, suna tsayawa tare.
Idan an karya amana, komawa na da wahala.

A KASUWANCI DA AIKI
Haɗin na da ƙarfi.
Ta**us yana kula da kuɗi da dorewa.
Scorpio yana kula da bincike, sirri da dabaru.
Za su iya gina abu mai girma idan babu rikicin iko.
DARASI NA RAYUWA
Ta**us yana koyon zurfin ji da sauya tsari idan ya dace.
Scorpio yana koyon haƙuri da sassauci.

GASKIYA A HIKIMA
Wannan haɗin mai ƙarfi ne sosai.
Akwai soyayya, aminci da dorewa.
Amma akwai kishi, taurin kai da rikici idan babu hikima.
Ba haɗin masu wasa ba ne.

A ƘARSHE
Taurari alamu ne kawai na halaye da yanayi.
Ba su da ikon tilasta soyayya, aure ko rabuwa.
Allah Shi kaɗai ne Mai iko da zukata da kaddara.
Abin da Ya so ne kaɗai yake tabbata.
Wallahu ta’ala a’alam.

Ibrahim fky al-falaky ✍️ 07033105536

10/04/2026

SIRRIN LOKACI DA TAURARI
Akwai wani kuskure da mutane da yawa ke yi ba tare da sun sani ba.
Suna zaton nasara tana fitowa ne daga ƙoƙari kawai.
Amma a ilimin taurari, ba haka abin yake ba.
Akwai lokacin da ƙoƙari kaɗai ba zai baka sakamako ba, komai irin ƙarfinsa. Kuma akwai lokacin da ƙaramin yunƙuri zai buɗe ƙofofi masu girma.
Me yasa hakan ke faruwa?
Saboda ba kai kaɗai kake motsa rayuwarka ba. Akwai tasirin taurari da suke tafiya da kai, suna buɗe maka hanya ko kuma suna takaita maka motsi ba tare da ka sani ba.

Akwai lokacin da taurari ke ƙarfafa fara abu. Idan ka yi anfani da wannan lokaci, abubuwa suna tafiya cikin sauƙi kamar an share maka hanya.
Amma idan ka yi kuskuren fara abu a lokacin da taurari ke nuna jinkiri, zaka iya shafe lokaci kana gwagwarmaya ba tare da ka fahimci dalili ba.

Ka taɓa yin tunanin:
Me yasa wani lokaci kake jin ƙarfin zuciya da kwarin gwiwa ba tare da wani dalili ba? Me yasa wani lokaci kuma komai ya yi nauyi a gare ka har ka kasa motsawa?
Wannan ba kawai yanayin zuciya bane. Sau da yawa yana da alaƙa da yadda taurari suke a wannan lokaci.

Akwai lokutan da ya dace ka fara kasuwanci
ka shiga wata mu’amala
ka yanke hukunci mai girma
Akwai kuma lokutan da ya kamata ka tsaya ka lura
ka jinkirta
ko ma ka kauce gaba ɗaya
Amma tambayar ita ce… ka san bambancin?
Idan baka sani ba, zaka iya shiga abu a lokacin da zai jawo maka asara. Ko kuma ka jinkirta abu a lokacin da zai iya zama nasara mai girma a gare ka.

Ilimin taurari ba wai don hasashe kawai bane. Hanya ce ta fahimtar lokacin da ya dace da kai.
Amma wannan yana buƙatar ka san abubuwa guda uku:
1 Burujinka
2 Yanayin taurarin da suke tasiri a kai
3 lokacin da waɗannan taurari ke aiki a rayuwarka
Ba kowa bane yake da wannan ilimi. Kuma ba kowa bane yake anfani da shi yadda ya kamata.
Amma wanda ya fahimci wannan sirri, yana fara ganin abubuwa daban.
Yana san lokacin da zai yi magana… da lokacin da zai yi shiru.
Yana san lokacin da zai ɗauki mataki… da lokacin da zai jira.
Kai fa?
Shin kana tafiya ne bisa fahimta… ko kuma kana tafiya ne kawai bisa ƙoƙari?
Idan kana son sanin yadda taurari suke tasiri a rayuwarka, to lokaci ya yi da zaka fara tambaya.

AƘARSHE
Taurari alamu ne kawai na halaye da yanayi.
Ba su da ikon sawa ko hanawa
Allah Shi kaɗai ne Mai iko da zukata da kaddara.
Abin da Ya so ne kaɗai yake tabbata.
Wallahu ta’ala a’alam.

Ibrahim fky al falaky ✍️ 07033105536

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address

Gombe

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 09:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Thursday 09:00 - 17:00
Friday 09:00 - 17:00
Saturday 09:00 - 17:00
Sunday 09:00 - 17:00