FC Yan Samari

FC Yan Samari

Share

FC Yan Samari Official Football Club Developing young talents, building future champions. Nigeria Unity • Discipline • Success ⚽ One Team, One Dream

13/07/2026

SANARWA GA DUKKAN MAGOYA BAYAN FC YAN SAMARI!💙⚽

Da farin ciki muke sanar da ku cewa FC YAN SAMARI ta samu gurbin shiga gasar GOMBE STATE FA Super League, tare da sauran kungiyoyi 31 da s**a cancanta. Wannan wata babbar dama ce a gare mu domin ci gaba da nuna ƙwazo da ɗaukaka sunan ƙungiyarmu.

Muna kira ga dukkan masoya, magoya baya da masu fatan alheri da su ci gaba da kasancewa tare da mu a wannan sabon ƙalubale. Goyon bayanku shi ne ƙarfafa mana gwiwa domin cimma manyan nasarori.

Mungode da irin soyayya da goyon bayan da kuke ba mu a ko da yaushe. Da yardar ALLAH, za mu yi iya bakin ƙoƙarinmu wajen faranta muku rai a wannan gasar.

FC YANSAMARI – Together We Rise! ⚽ Gombe State FA Super League... Muna zuwa!💪🔥

28/06/2026

SAKO GA MASOYAN FC YAN SAMARI

Alhamdulillah a kan komai.

Ko dayake tafiyarmu a State League ta zo ƙarshe, muna miƙa saƙon godiya ta musamman gare ku, masoyanmu na kusa da na nesa. Goyon bayanku, addu'o'inku, da ƙarfafawar da kuka bamu tun daga farkon gasar har zuwa yau sun kasance babban abin alfahari a gare mu.

Mun yi bakin ƙoƙarinmu a kowace wasa, amma ƙaddarar Allah ita ce mafi alheri. Mun karɓi wannan sakamako cikin tawakkali, kuma za mu dawo da ƙarfi, ƙwarewa, da sabon azama.

Muna roƙon Allah (SWT) Ya saka muku da alheri bisa irin ƙaunar da kuka nuna mana. Ku ci gaba da kasancewa tare da mu, domin wannan ba ƙarshen tafiya ba ne, farkon wani sabon babi ne.

Mungode sosai da goyon bayanku. In Sha Allah, FC YAN SAMARI zata dawo da ƙarfi fiye da da.🤍⚽

A nasara da rashin nasara, tare da ku muke alfahari.

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address

Gombe
760001