Maitama quarters Gombe
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Maitama quarters Gombe, Real Estate, Maitama opposite high Court gombe, Gombe.
26/10/2023
10/10/2023
MASHA ALLAH:🙏🙏🙏
Allah Yasa Muga Annabi Muhammadu (S.A.W), Allah Ya Biyawa Kowa Bukatansa Na Alkairi, Allah Yasa Mugama Da Duniya Lafiya, Allah Ya Bamu Albarkan Dake Cikin Wannan Rana.
Ina Muku Fatan Alheri.🙏🙏🙏
10/10/2023
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
ADDU'ARMU AWANNAN SAFIYAR
Da albarkar sunan Allah mai Rahama Mai jin Qai, Salati da aminci su tabbata bisa Annabin Rahama, Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa baki daya.
Ya Allah kai Mai Afuwa ne, kana son yin Afuwa. To kayi mana afuwa. Ka gafarta mana dukkan laifukanmu manyansu da Qananansu. Wadanda muka sani da wadanda bamu sani ba. Da wadanda muka aikata afili ko aboye. Da wadanda mukayi cikin kuskure ko da gangan.
Ka gafarta ma Mahaifanmu da Malumanmu da 'Qannenmu da yayyenmu da danginmu. Da rayayyunmu da Matattaunmu da Mazajenmu da Matayenmu da Qanananmu da Manyanmu.
Ya Allah ba don isarmu ba, sai dai don falalarka da rahamarka wacce ta yalwaci dukkan Halittunka baki daya. Ka kiyayemu daga sharrukan fili da na boye, da Bala'o'i da Musibu da miyagun abubuwan da muka sani da wadanda bamu sani ba. Da wadanda muka ta'ba rokon kiyayewarka daga garesu, har wadanda ma bamu ta'ba neman tsari daga garesu ba. Harma wadanda bamu san yadda ake neman tsarinka daga garesu ba.
Ya Allah ka sadamu da dukkan alkhairai da Falaloli da Baiwa da rahama da yalwatuwa anan duniya da Alqiyamah. Ka bamu mafi girman Kaso daga kowacce gafara da rahama da baiwa da girmamawa wace kake yi ma bayinka awatan Ramadhana baki daya.
Ya Allah dukkan abinda zaka bamu, ka bamu mafi albarka mafi tsarki mafi alkhairi. Kada ka jarrabemu da irin abinda ka Jarrabi wadanda suke kafinmu.
Ya Allah ka bamu duk irin sakamakon da kake yiwa masu son juna dominka, Kuma muna tawassuli da Soyayyar da muke yiwa Annabinka Zababbenka Shugabanmu Annabi Muhammadu (S.A.W) don wannan kada ka ta'bar da abinda muke fata.
Kai Mai Karamci ne. Kai Girma ne. Kai Ka'dai kake da iko da Mulki da hukunci da Buwaya da Martabobi
Rokonmu shine Kayi Salati da Aminci bisa mafi soyuwar bayinka gareka, Annabinmu Shugabanmu Muhammadu tare da iyalan gidansa da Sahabbansa gwargwadon darajarsa da martabarsa da fifikonsa da Muqamansa masu girma awajenka. Ameeen.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Gombe