Al Amsal

Al Amsal

Share

|Digital Marketing|
|Science|
|Technology|

24/07/2026

Duk wanda ya ganeta shima mutumin banza ne 😂

17/07/2026

YA KAMATA KUSANI AKAN SHIRIN RENEWED HOPE VOCATIONAL AND SKILLS TRAINING PROGRAMME (VSTP)!!!

1. VSTP Shirine Na Gwamnatin Tarayya A Karkashin Federal Ministry Of Humanitarian Affairs And Poverty Reduction, A Karkashin Kulawar NSIPA.

2. Shirin Zai Tallafawa Matasa Mutum 18,510 Ta Hanyar Koya Musu Sana'a Da Kuma Basu Kayan Aiki Da Zaran An Gama Koyar Dasu Domin Su Dogara Da Kansu.

4. Ana Bukatar Email, Phone Number, BVN Da NIN Domin Yin Rigista.

5. Za'ayi Training A Federal And State Technical Colleges Na Kowace Jaha.

6. Za'ayi Training Ne Akan Sana'o'i 14 Na Zamani. Ga Sana'o'in:

a. Automobile Technology
b. Agricultural Technology
c. Banking And Confectionary
d. Carpentry
e. Catering Services
f. Electrical Installation
g. Housekeeping
h. Jewelry And Bead Making
i. Masonry
j. Plumbing
k. Welding And Fabrication
l. Fashion Design And Sewing
m. Grinding Machine Operations
n. Vulcanizing And Tyre Services.

7. Da Zaran An Gama Training Za'a Bada Certificate Da Starter Packs.

8. Duk Wanda Ya Samu Shiga Cikin Shirin VSTP, To Zai Samu Alkhairi Dumu Dumu.

9. A Yanxu Application Din Baya Tafiya Amma Zai Iya Ci Gaba Da Tafiya A Kowani Lokaci.

Mu Kasance Tare Domin Samun Sahihan Labarai Akan Duk Wata Program Na Gwamnatin Tarayya.

Ga Link a Comment section 👇

Photos from Al Amsal's post 17/07/2026

KOTUN DAUKAKA ƘARA TA SOKE WASU MUHIMMAN SASHE NA DOKAR ZAƁE TA 2026.

Abuja – Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta yanke hukuncin soke wasu muhimman tanade-tanade na Dokar Zaɓe ta 2026 da s**a shafi rajistar mambobin jam'iyyun siyasa da kuma tsarin zaɓen 'yan takara, bayan ta bayyana cewa sun saɓa wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999.

Hukuncin ya fito ne daga kwamitin alkalai uku na Kotun Ɗaukaka Ƙara ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Balkisu Aliyu, inda kotun baki ɗaya ta amince da ƙarar da Jam'iyyar Zenith ta shigar mai lamba CA/ABJ/CV/750/2026, tare da soke hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke a baya na yin watsi da ƙarar.

A cikin hukuncin da Mai Shari'a Eberechi Nyesom-Wike ta karanta, kotun ta ayyana cewa sashe na 77(5), 77(6), 77(7), da 84(2) na Dokar Zaɓe ta 2026 sun ci karo da Kundin Tsarin Mulki, don haka ba su da inganci.

Kotun ta bayyana cewa Majalisar Tarayya ba ta da ikon ƙaƙaba wa jam'iyyun siyasa wasu ƙuntatawa ta hanyar doka, idan waɗannan ƙuntatawar sun saɓa da haƙƙoƙin da Kundin Tsarin Mulki ya riga ya ba su.

Haka kuma, kotun ta jaddada cewa sashe na 221 da 222 na Kundin Tsarin Mulki sun tanadi cewa jam'iyyun siyasa ne ke da alhakin tsayar da 'yan takara domin shiga zaɓe tare da gudanar da harkokinsu na cikin gida.

Kotun ta ƙara da cewa, idan Kundin Tsarin Mulki ya riga ya fayyace sharuddan cancanta da rashin cancanta ga masu neman muƙaman siyasa, Dokar Zaɓe ba za ta iya ƙara wasu sababbin sharudda da za su hana mutum mai cikakkiyar cancanta shiga zaɓen fidda gwani na jam'iyya ba.

Wannan ƙara ta samo asali ne daga hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja wanda Mai Shari'a Mohammed Umar ya yanke a ranar 5 ga Mayu, 2026, inda ya yi watsi da ƙarar da Jam'iyyar Zenith ta shigar tana ƙalubalantar sahihancin waɗannan tanade-tanade na Dokar Zaɓe.

Daga cikin sassan da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke akwai Sashe na 77(5), wanda ya tanadi cewa mambobin jam'iyya waɗanda sunayensu kaɗai ke cikin rajistar da aka miƙa wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ne za su iya kaɗa ƙuri'a ko kuma a zaɓe su a zaɓen fidda gwani, tarukan jam'iyya da manyan tarukan ƙasa.

Hakazalika, kotun ta soke Sashe na 77(6), wanda ya hana jam'iyyun siyasa amfani da wata rajistar mambobi banda wadda aka riga aka miƙa wa INEC, inda kotun ta bayyana cewa wannan tanadi ya bai wa dokar ikon da ya wuce abin da Kundin Tsarin Mulki ya amince da shi.

©️©️ Al-Amsal

13/07/2026

Wasu suna wasa da shirin nan na bada training akan sanya mita watau PRESIDENTIAL METERING INITIATIVE (PMI).

Bari kuji idan aka baka training ɗin nan sannan ka samu satifiket na wannan shiri toh kuɗin da zaka samu suna da yawa a duk rana.

Shin kun san ko nawa mutum zai samu idan yana sanya meter guda biyar a duk rana, kuɗi ne masu yawa.

Kada ku yi wasa da wannan damar musamman waɗanda aka basu stream 1 da kuma stream 2 da kuma stream 3.
Waɗanda basu cike ba su dage su cike.

Idan kasan ɗan uwanka bai cike ba ko kuma bai iya cikewa ba toh dan Allah ka taimaka ka cike mashi, kayi ma mutane hanyar aikin alkhairi abu ne mai kyau.

Wanda ya ke da wata tambaya yayi a kwament sekshen.

Allah ya bada Sa'a.

Want your business to be the top-listed Media Company in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address

Gombe