Gure Properties
Gure Properties is Nigeria’s trusted digital marketplace for verified real estate. Find homes, land, and shops for sale or rent across Nigeria.
25/06/2026
Gina gida yana dagacikin abunda ke karye matasan Katsina, Sokoto, Kebbi da Zamfara
Menene dalili?
Mafiyawan iyayenmu basa baka aure har sai idan ka gina gida, wannan abun yazamo al’ada awurinmu
Idan kana zaune a gidan haya, tamkar cin zarafi ne awurin iyayen budurwa da yan uwanta
Shiyasa kowane matashi idan yataso, babban burinsa shine ya gina gida, ya siye roba-roba, yayi aure 👌
Babu wani tunanin gobe ko makomar iyali
—————————————
Idan zaka gina gida mai ɗakin mata biyu ko uku, sai ka kashe kuɗi kamar haka:
1. Matsakaici na talakawa (5 to 10 million)
2. Mai dama (15 million)
3. Na alfarma (20 million zuwa 50 million ko fiye da haka)
—————————————
Dalilin da yasa matasan Kano, Kaduna, Abuja, Lagos da wasu jihohin s**a tsere mana shine:
Idan matashi ya mallake kuɗi wanda adadinsu yakai N2,000,000 ba gini suke farawa ba
Ƙoƙari suke suyi kasuwanci da wannan kuɗin
Sai kaga matashi yana rayuwa a gidan haya, amma yanada jarin naira miliyan 30, ko fiye da haka
Ba ruwansu da maula a gidajen yan siyasa, ko ganin laifin gwamnati.
————————————
Amma a wurinmu sai kaga matashi yafara aikin gini da N500,000 amma bayada jarin N100,000 a kasuwa
Yakamata mu canza wannan tsarin, idan bahaka ba zamucigaba da fuskantar koma baya da zama cikin jerin wanda ke fama da talauci a jihohin arewa 🥹
Wanda yaga laifina, yayi afwa 🙏
Daga Alhassan Mai Lafiya
S A W��
Ku Yawaita Kyauta Ku Rage Bada Aro, Saboda Aro Yana Yanke Zumunci Kyauta Kuma Na Ƙulla Zumunci!
17/06/2026
Bayan birnin tarayya Abuja wace jahace tafi tsada a gidan haya ?
Saurara kaji 🧏♂️
Click here to claim your Sponsored Listing.
Website
Address
Gombe