HALADU BAJOGA

HALADU BAJOGA

Share

Na bude wannan page ne don ci gaba da saduwa da abokai daga kowane sashi na duniya. Don haka kai tsaye ka ziyarci shafi na.

10/03/2026

SHUGABANCIN MACE A MUSULUNCI:

1. Malaman Musulunci sun yi sabani a kan halaccin shugabancin mace, dalilin wannan sabani nasu kuwa shi ne irin yadda fahimtarsu ta saba wa juna game da wani ingantaccen hadithin Annabi mai tsira da amincin Allah, Hadithi na 4425 wanda Imamul Bukhari ya ruwaito daga Sahabi Abuu Bakrah ya ce:-
((لقد نفعني الله بكلمة سمعتها من رسول الله صلى الله عليه وسلم ايام الجمل بعد ما كدت ان الحق بأصحاب الجمل فاقاتل معهم. قال: لما بلغ رسول الله صلى الله عليه وسلم ان أهل فارس قد ملكوا عليهم بنت كسرى قال: لن يفلح قوم ولوا أمرهم امرأة))
Ma’ana: ((Hakika Allah Ya amfane ni da wata kalma da na ji daga Manzon Allah mai tsira da amincin Allah a kwanukan Jamal bayan na yi kusa in fada cikin sahun mutanen Jamal in yi yaki tare da su.

Ya ce: Lokacin da labari ya riski Manzon Allah mai tsira da amincin Allah cewa mutanen Farisa sun nada wa kansu Yar Kisraa a matsayin sauniyarsu sai ya ce: “Ba za su rabauta ba mutanen da s**a jagorantar da wata mace lamarinsu)).

Masanin ilmin Hadithi Al-Haafiz Ibnu Hajar ya ce cikin littafinsa Fathul Baarii 7/735 a lokacin da yake yi wa wannan Hadithi sharhi:-
((والمنع من ان تلي الإمارة والقضاء قول الجمهور، وأجازه الطبري، وهي رواية عن مالك، وعن ابي حنيفة تلي الحكم فيما تجوز فيه شهادة النساء)).

Ma’ana: ((Hana mace ta jibinci Mulki da Alkalanci magana ce ta masu rinjaye cikin Malamai.

Amma (Imaamut) Tabarii ya halatta hakan, haka nan wata riwayar fatawa ma daga (Imamu) Maalik.

Daga Abuu Hanifah kuwa mace tana iya yin Alkalanci cikin mas’alolin da ake karbar shidar mata a cikinsu)).

2. A mazhabar Hanafiyyah halal ne mace ta yi sarutar da za a rika kiran ta Suldan, saboda ya zo cikin babban littafin mazhabar Hanafiyyah mai suna Al-Bahrur Raa’q 7/5 wanda Imam Ibnu Nujaim ya wallafa kamar haka:-
((وأما سلطنتها فصحيحة؛ وقد ولي مصر إمرة تسمى شجرة الدر جارية الملك الصالح بن أيوب)).

Ma’ana: ((Amma Saldanarta (watau mace ta yi saruatar da za a rika kiranta Sultan) to wannan kam ingantacce ne, saboda wata mace mai suna Shajaratud

08/01/2026

JIYA BA YAU BA...

Shugaban Ƙasar Amurka, President John F. Kennedy, tare da Firayim Ministan Najeriya, Sir Abubakar Tafawa Balewa, a Fadar White House, dake Washington D.C., yayin wata ziyara ta musamman da Sir Abubakar Tafawa Balewa ya kai Amurka a watan Yuli, na Shekarar 1961.

Masana tarihi sun bayyana cewa wannan ita ce haduwarsu ta ƙarshe, domin daga baya aka kashe President John F. Kennedy a watan Nuwamba, 1963, yayin da shi kuma Sir Abubakar Tafawa Balewa aka kashe shi a ranar 15 ga Janairu, na Shekarar 1966, a lokacin juyin mulkin soji na farko a Najeriya.

Ya Allah Ka jiƙan Sir Abubakar Tafawa Balewa, tare da sauran magabatanmu, Ka gafarta musu kurakuransu, Ka sanya Aljanna ta zama makomarsu. Ameen.

06/12/2025

Wata yar Fulani mai tallan nono a yalwan yawuri 1961. Yau Shekaru (64) kenan.

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Address

Bajoga
Gombe