Gada Biyu Community Engagement and Development Initiative

Gada Biyu Community Engagement and Development Initiative

Share

CSDP Additional Financing is a world Bank Assisted Project that promotes Community Driven Development in Nigeria.

09/02/2026

Bankin Masana’antu na Najeriya (BoI) ya samu amincewar Hukumar Babban Bankin Najeriya (CBN) domin fara gudanar da bada Rance maras Ruwa (Non-Interest Banking), lamarin da ke nuna babban ci gaba a tsarin samar da kuɗaɗen tallafi na bankin.

Shugaban Bankin, Dakta Olasupo Olusi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Wannan amincewa ana sa ran za ta ƙara ƙarfafa rawar da BoI ke takawa wajen bunƙasa ci gaban masana’antu mai ɗorewa, tare da faɗaɗa damar samun jari ga ƙananan da matsakaitan ’yan kasuwa, da sauran sassan kasuwanci masu tasiri waɗanda ba su da sauƙin samun rance a baya.

Da wannan izini, BoI zai fara bayar da Rance Maras Ruwa, wanda ya dogara da tsarin kuɗi na gaskiya da haɗin kai (risk-sharing), tare da hana karɓar riba (interest).

Tsarin zai mayar da hankali kan ba da tallafin kuɗi bisa kadarori (asset-backed financing) domin tallafa wa ci gaban kasuwanci da masana’antu a faɗin ƙasar nan.

Credit
Punch news

Want your organization to be the top-listed Non Profit Organization in Gusau?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address

Sokoto Road
Gusau