Sports Hausa News
Sports Hausa News shafi ne da ke kawo muku labaran wasanni da harshen Hausa akan lokaci.
28/05/2026
🚨🫡 Joan Laporta da kansa ya shiga cikin tattaunawa domin taimakawa wajen kammala komawar Anthony Gordon zuwa FC Barcelona, kamar yadda BILD ta ruwaito. 🤝🏻🔵🔴
🔴 FC Bayern Munich ta shafe makonni tana tattaunawa da Gordon da Newcastle United, amma ƙarancin tayinsu da jinkirin tattaunawa ya bai wa Barça damar matsawa da sauri. ⏳
Laporta ya yi magana kai tsaye da Gordon domin tabbatar masa da muhimmancin sa ga kulob ɗin da kuma kwantar masa da hankali kan batun rajista. ✍️
Haka kuma Hansi Flick ya taka muhimmiyar rawa wajen jan hankalin ɗan wasan. 🔥
💰 Rahotanni sun ce Newcastle na iya samun sama da €80M idan duk bonus/add-ons s**a cika, kuma za a biya kuɗin a sannu-sannu.
28/05/2026
🚨📅 A irin wannan ranar a shekarar 2017 Francesco Totti ya buga wasansa na ƙarshe a tarihin AS Roma. 👑
📊 Tarihinsa a AS Roma:
◉ Wasanni 786
◉ Ƙwallaye 307
◉ Kofuna 5 🏆
👑 An masa laƙabi da “The King of Rome” — gwarzon da ya sadaukar da dukkan rayuwar kwallon kafa ga kulob guda ɗaya. ❤️💛
28/05/2026
🚨🇪🇸 Mafarkin Sergio Ramos na sayen kulob ɗin Sevilla ya zo ƙarshe. 📉💔
Sevilla FC ta dakatar da tattaunawar saye a hukumance bayan Ramos da tawagarsa ta masu zuba jari sun gabatar da sabon tayin da ya yi ƙasa sosai da wanda aka fara tattaunawa a kai da safiyar yau. 💵❌
Click here to claim your Sponsored Listing.
Website
Address
Hadejia