KGN Hausa

KGN Hausa

Share

KNG HAUSA jarida ce da ke kawo muku sahihan labarai masu muhimmanci wajen sanar da al'umma abubuwan da ke faru a ciki da wajen kasar Najeriya

20/05/2026

Mai neman jam’iyyar ADC ta tsayar da shi takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Niger mai wakiltar mazaɓar Kwantagora 1, Hon. Hamza Abdullahi, ya nemi goyon bayan ƴaƴan jam’iyyar tare da al’ummar mazaɓar domin samun nasarar tsayawa takara da kuma kai jam’iyyar ga cin nasara a zaɓe mai zuwa.

Hon. Hamza Abdullahi ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya aikowa TTN Hausa, inda ya ce yana da cikakken ƙuduri da shirye-shiryen yi wa al’ummar Kwantagora 1 hidima ta gaskiya idan har jam’iyyar ta amince da shi a matsayin ɗan takara.

Ya ce babban burinsa shi ne ganin an samar da wakilci nagari wanda zai kare muradun matasa, mata da sauran al’ummar mazaɓar a Majalisar Dokokin Jihar Niger.

A cewarsa, lokaci ya yi da za a bai wa mutane shugabanci mai cike da gaskiya da riƙon amana domin kawo ci gaba mai ɗorewa ga yankin.

“Na fito ne domin yi wa al’ummata hidima ba tare da son rai ko nuna bambanci ba. Ina mai tabbatar wa da ƴan jam’iyyar ADC da mutanen Kwantagora 1 cewa ba zan ba su kunya ba idan aka ba ni dama,” in ji shi.

Hon. Hamza ya kuma yi alƙawarin cewa zai yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen haɗa kan ƴaƴan jam’iyyar ADC tare da neman amincewar al’ummar mazaɓar domin jam’iyyar ta samu gagarumar nasara a dukkan matakan zaɓe.

Ya ƙara da cewa zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da shugabannin jam’iyya da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da an gudanar da siyasa cikin lumana, haɗin kai da mutunta juna.

Ɗan takarar ya kuma buƙaci magoya bayan jam’iyyar da matasa da su ci gaba da ba shi haɗin kai da addu’o’i domin cimma burin da aka sanya a gaba.

Ya ce nasarar ADC a Kwantagora 1 za ta zama wata sabuwar kafa ta ci gaba da inganta rayuwar al’umma a yankin.

A ƙarshe, Hon. Hamza Abdullahi ya jaddada cewa idan aka zaɓe shi, zai mayar da hankali wajen kawo ayyukan ci gaba, inganta walwalar jama’a da kuma tabbatar da cewa muryar mutanen Kwantagora 1 ta samu wakilci nagari a Majalisar Dokokin Jihar Niger.

05/05/2026
04/05/2026

I got over 50 reactions on my posts last week! Thanks everyone for your support! 🎉

04/05/2026

Hukumar alhazai ta jihar jigawa ta fara daukar sahun farko na maniyatanta a yau litinin.

04/05/2026

A jihar jigawa ana cigaba da gudanar da tantance yan takarkaru domin samun shugabanni da s**a cancanta wajen zama yan takarkaru a zaben 2027.

Shin wanne Dan takara kake fata ya zama gwaninka?

26/04/2026

Yayin da zaben 2027 ke ci gaba da karatowa 'yan hamayya a Najeriya, daga jam'iyyun siyasa sama da goma, sun karkakata hankalinsu wajen tattara karfinsu wuri guda domin tunkarar shugaba Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC.

Yayin wani gangamin jam'iyyun hamayya da aka gudanar a karshen mako a birnin Badun na jihar Oyo, jam'iyuun PDP da ADC, da Labour da kuma NNPP sun yi imaninn ba abu ne mai yiwuwa a iya kayar da shugaba Tinubu idan aka ki hada kai ba, saboda a cewarsu ''Yadda shugaba Tinubu ke amfani da karfin mulki wajen murkushe dimukradiyya''

Dukkan wadanda s**a gabatar da jawabi a yarin taron sun yi tsokaci kan muhimmancin jingine bukatar kashin kai, ko ta yin takara don ganin an yi aiki tare wajen samar da kwakkwaran dan takara da zai iya jan zare da Tinubun a zaben da ke tafe.

Mahalata taron sun hadar da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan Anambra Peter Obi da tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso da tsohon gwamnan Rivers Rotimi Amaechi da sauran wasu kusoshin hamayya.

Jam'iyyun da s**a halarci taron sun hadar da ADC, da PDP, da Labour, da NNPP, da PRP, da Accord, da APM, da (YP), da ADP, da sauransu

26/04/2026

A wani taron duba hanyoyin magance rikice-rikice da matsalolin da ke haddasa ficewar mambobin Jam’iyyar APC a Jihar Jigawa, wanda gwamnatin jihar ta shirya a makon da ya gabata a birnin Dutse, an tattauna batutuwa masu muhimmanci.

Gwamnan Jihar, Umar Namadi Danmodi, ya bayyana cewa kuɗaɗen da ake bai wa wasu daga cikin ma’aikata da masu ruwa da tsaki na kusa da shi na kaiwa tsakanin naira 100,000 zuwa 200,000 a kowane wata.

Ya danganta hakan da ƙoƙarinsa na rage matsin rayuwa, yana mai cewa rashin aiki tukuru na daga cikin abubuwan da ke haifar da ficewar wasu mambobin jam’iyyar daga APC zuwa ADC.

Ya ƙara da cewa bai kamata a riƙa samun ficewa daga jam’iyyar ba, duba da irin ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi wajen inganta jin daɗin ma’aikata bisa la’akari da albashin da suke karɓa.
Sai dai tambaya ita ce:

Shin irin waɗannan kuɗaɗe da ma’aikatan gwamnati ke samu na iya hana ko rage ficewar mambobin jam’iyyar APC zuwa ADC?

Haka kuma, mene ne ainihin dalilan da ke sa wasu ke barin jam’iyyarsu a jihar?

25/04/2026

Yadda aka gudanar da bikin samun yancin masarautar Hadejia da ke jihar Jigawa a cikarta shekarar 120 daga turawan Birtaniya.

25/04/2026

Gwamnatin Jihar Jigawa ta kaddamar da rabon risho guda dubu goma kyauta ga al’umma domin rage sare itatuwa da yaki da matsalar sauyin yanayi

Rahotanni daga Jihar Jigawa kamar yadda Arewa Updates ta rawaito sun bayyana cewa, Kwamishinan Lantarki da Makamashi na jihar Malam Surajo Musa ne ya sanar da hakan a wajen bikin yaye matasa da s**a samu horo kan yin risho da wata kungiya ta shirya a garin Baranda.

Ya ce, shirin na daga cikin matakan da gwamnati ke dauka domin dakile kwararowar hamada da kare muhalli.

Haka kuma, ya bayyana cewa tuni gwamnati ta mayar da wasu ayyukan ma’aikatu da hukumomi da fitilun kan t**i a wasu hedikwatocin kananan hukumomi 11 zuwa masu amfani da hasken rana, tare da samar da kananan tashoshin wuta a kauyuka da makarantun Tsangaya.

A nasa bangare, Daraktan shirin Elip Pace Initiative Malam Isa Mustapha ya ce an zabo matasa daga kananan hukumomi tare da basu horo kan sarrafa gawayi da kuma yin risho domin rage gurbatar muhalli.

Shin kuna cikin waɗanda s**a rabauta da wannan tallafi?

Want your business to be the top-listed Media Company in Hadejia?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address

Jigawa
Hadejia