Hadejia Emirate Youth Forum
...in God (alone) I seek refuge UNITED WE STAND!
07/10/2022
002
ZALUNCIN HUKUMAR RAYA FADAMUN KOGUNAN HADEJIA- JAMA'ARE
YUNKURIN NEMAN HAKKI.
KURA DA SHAN BUGU, GARDI DA AMSHE ABINCI.
Halin da manoman Kasar Hadejia da kuma al'ummar da ke da mazauni a ga6ar Kogin Hadejia suke ciki kenan. Hukumar (HJRVDA) ce da ke da alhakin tattara ruwan da adana shi da kuma rabawa don amfanin manoma musamman a lokacin aikin RANI. Wannan Hukuma ce ke da alhakin YASHE KOGUNAN don ruwan ya samu saukin shigewa zuwa Jihar Yobe, Borno da wani yanki na KAMARU da CHADI, amma ta gaza yin hakan a shekaru da dama da s**a shude, alhali tana da ikon sakin ruwan don amfanin manoma, amma abun takaici manoma da yawa sun dogara da tona rijiya da sayen INJI da man FETUR ko DIESEL don shayar da gonakin su. Hakan yana faruwa a muhallin da Hukumar take bayarwa haya don ayi noman, amma don tsabar mugunta ba zasu saki ruwan ba sun karkata don amfanin wata Jihar na samun hasken lantarki, wanda ba hakane ainihin dalilin yin MADATSAR RUWAN ba.
Babu hujja a ajiye ruwan da yakamata a sakar mana muyi amfani da shi a lokacin da muke bukata amma sai a hana kuma a sako shi a lokacin da bamu bukatar sa yana haifar mana asarar RAYUKA, MUHALLI da kuma GONAKI.
Bai kyautu mu zuba ido irin wannan 6arna tana faruwa duk shekara ba. Ana tauye TATTALIN ARZUKIN mu ne ta yin hasarar rayuka, muhalli, gonaki da kuma dabbobi.
Ku tashi mu farka HADEJIAWA mu KALUBALANCI aiyukan wannan HUKUMA na zalunchi da take aiwatarwa a muhallin mu.
Wani abun lura shine inda ake TATTARA RUWAN baya musu BARNA sai MU da muke bukatar sa a lokacin aikin RANI ake hana mu, kuma a sake shi lokacin da bamu bukatar sa.
A karshe muna sake sanar da yan uwa MANOMA musamman na KASAR HADEJIA cewa muna ci gaba da tattara bayanai akan yawan asarar da muka yi don GURFANAR da wannan HUKUMA gaban KULIYA MANTA SABO.
Dr Isah Billami Hadejia ,
Manomi, Dan kasuwa,
Mai gwagwarmayar neman hakkin al'umma.
Click here to claim your Sponsored Listing.