Rigasa Reporters News
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Rigasa Reporters News, Writer, Kaduna.
25/05/2026
Lokutan Sallah Idi Babban
Sanarwar daga Shugaban Kungiyar Izala ta Rigasa Karkashin Jagorancin Mal Abu Sufyan da Kwamitin sa,
Sun saka lokutan sallar Idi bana 1447 A.H 9:00am
Dafatan za'ayi sallah lafiya.
23/05/2026
BA BELLO KADAI NAYI ZABE BA 2023.
Inji: Hon Samaila Farar Aniya.
Tsohon ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kaduna North, Samaila Farar Aniya ya bayyana cewa zaben 2023 da aka yi bai tsaya kan mutum ɗaya ba, illa haɗin kai da goyon bayan gwamnati da al’umma gaba ɗaya.
A cewarsa:
“Bada Bello kaɗai na zabe ba a 2023. Ni da Bello da Gwamnatin Jihar Kaduna da kuma jama’a muka yi zaɓe tare a wancan lokacin.”
Ya ƙara da cewa an nuna wa Bello gata sosai a lokacin zaɓen, amma yanzu siyasa ta canja salo.
“A wannan karon, tsakanina da Bello ne za a yi zaɓe kai tsaye. Babu maganar gatar da ya samu k**ar yadda aka yi a 2023.”
Wannan furuci na Hon. Farar Aniya na nuni da cewa siyasar Kaduna North na 2027 za ta kasance mai zafi da ɗaukar hankali,
musamman ganin yadda manyan jiga-jigai ke fara bayyana matsayinsu tun kafin lokacin zaɓe ya ƙarato.
Tambaya Ga Jama’a:
Shin kuna ganin wannan magana ta Hon. Farar Aniya na nuna ƙarfin siyasa ne, ko kuwa alamar sabuwar takaddama ce tsakanin sa da Bello a tunkarar zaɓen 2027?
19/05/2026
Idan Shi Aka Ba, Zan Bi Shi — Idan Ni Aka Ba, Zai Bi Ni” 🔥
Wannan kalamai daga Rt, Hon Zailani da Sen, Shehu sani sun dauki hankalin mutane bayan zaben fidda gwani.
Sai dai tambayar da mutane da dama suke yi ita ce: Shin wannan hadin kai zai dore bayan an bayyana wanda ya samu tikiti? 🤔
A siyasa, kalamai masu dadi suna da muhimmanci, amma abin da jama’a s**a fi so shi ne ganin hadin kai da aiki tare a aikace, ba kawai a baki ba.
Idan har wannan alkawari ya tabbata, zai iya zama babban darasi ga sauran ‘yan siyasa cewa siyasa ba fada ba ce, siyasa hadin kai ce da mutunta juna domin cigaban al’umma.
Rigasa reporters news
Click here to claim your Sponsored Listing.