Gwale LGA Development Association

Gwale LGA Development Association

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Gwale LGA Development Association, Community Organization, 260, Sani Mainagge, Kano.

14/11/2025

SHUGABAN AMURKA YAYI MARTANI GA ƳAN NAJERIYA:

Martanin Trump gameda ɗabi'un ƴan Najeriya na Barkwanchi a lokachin da wani ƙalubale ya tunkaresu.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana ƴan Najeriya a matsayin "manyan mutane da ke maida komai barkwanchi ko da a lokachin da s**a tsinchi kansu a chikin firgichi.

Yayin magana da wasu jakadun Najeriya a Amurka, Donald Trump ya che:

“Najeriya che ƙasa ta farko da ya sani wacche za ta samu labarin yaƙi ya tunkarota mutanen chiki su fara yin raha da barkwanchi. Wannan abun mamaki ne matuƙa gaya. Ƴan Najeriya mutane ne masu daraja, amma ba sa ɗaukar komai da muhimmanchi, komai abun raha ne a wurinsu.”

Shugaban ya nuna mamakinsa kan yadda ƴan Najeriya ke amfani da barkwanchi wajen fuskantar matsalolin duniya maimakon firgichi ko tsoro.

Ya kara da chewa:

"Ban taɓa ganin mutane masu irin wannan ɗabi'a ba. Sauran ƙasashe firgita suke in s**a ji amon muryar mu, amma su kuma ƴan Najeriya abun wasa s**a mayar damu wannan kam abin ban dariya ne, amma kuma abin mamaki.”

Photos from Gwale LGA Development Association's post 11/10/2025

Shugaba Tinubu Ya Yi Wa Maryam Sanda Afuwa Domin Ta Cigaba Da Kula Da 'Yaŕtà, Bayan Zàrgiñta Da Kàshè Mìjintà
..ga jerin sunayen wadanda Gwamnatin Shugaba Tinubu ta yi wa Afuwa da Sassauci kan hukuncin da aka zartar musu.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bai wa manyan fursunoni da tsofaffin fursunoni guda 175 afuwa da sassauci, ciki har da marigayi Major Janar Mamman Jiya Vatsa, marigayi Ken Saro-Wiwa, “Ogoni Nine”, tare da Maryam Sanda da wasu da dama.

Kwamitin bada shawara kan afuwar shugaban ƙasa, ƙarƙashin jagorancin Ministan Shari’a, Prince Lateef Olasunkanmi Fagbemi ne ya bada shawarar yin afuwa ga tsofaffin fursunoni 15 (11 daga cikinsu sun riga sun rasu), da bayar da sassauci ga fursunoni 82, tare da rage wa’adi ga fursunoni 65. Haka kuma, an mayar da hukuncin kisa ga fursunoni bakwai zuwa daurin rai-da-rai.

Prince Fagbemi ya gabatar da wannan rahoto a taron Council of State ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Cikakken Sunayen Waɗanda S**a Amfana da Afuwa da Sassauci

Waɗanda Aka Yi Wa Afuwa
1. Nweke Francis Chibueze (44) – daurin rai-da-rai saboda kwayar Co***ne.
2. Dr Nwogu Peters (67) – hukuncin shekara 17 saboda zamba tun 2013.
3. Mrs Anastasia Daniel Nwaoba (63) – ta rigaya ta kammala zaman gidan yari saboda zamba.
4. Barr. Hussaini Alhaji Umar (58) – an yanke masa tara N150M a shari’ar ICPC a 2023.
5. Ayinla Saadu Alanamu (63) – an yanke masa shekara 7 saboda cin hanci a 2019.
6. Hon. Farouk M. Lawan (62) – an yanke masa shekara 5 saboda rashawa a 2021.

Waɗanda Aka Yi Wa Afuwa Bayan Mutuwarsu

7. Sir Herbert Macaulay – an hana shi mukaman siyasa a 1913 saboda zargin karkatar da kuɗi ta hannun Turawan mulkin mallaka.
8. Major Janar Mamman Jiya Vatsa – an kashe shi a 1986 saboda zargin juyin mulki.

Ogoni Nine
9. Ken Saro-Wiwa
10. Saturday Dobee
11. Nordu Eawa
12. Daniel Gbooko
13. Paul Levera
14. Felix Nuate
15. Baribor Bera
16. Barinem Kiobel
17. John Kpuine

An kuma yi girmamawa ta musamman ga waɗanda aka kashe a wannan rikici:
• Ch

09/10/2025

ZABEN 2027: Ko Kana Daga Cikin Kanawan Da Za Su Sake Zabar Gwamna Abba Kabir A Karo Na Biyu?

08/10/2025

KAI DUNIYA!
Tiyata ne akayi ta ujila(emergency) kuma na haihuwane.
Amma kash abinda aka cire babu rai.
Kafin a fara aikin saida ta tambayeni 'likita zaizo da rai kuwa?'
Na bata karfin gwiwan cewa yanzu babban damuwanmu mu ceci ranta ne amma muna fatan samun babyn ( scanning ya nuna babu rai).
Shiganmu ciki mun sami babban matsala, mahaifan ta fashe tayi dagadaga yanda ba zata dinku ba sai dai a cireta gabadaya.
Babban matsalan shine haifuwanta na ukune duk ba rai.
Na farko ta haihu a gida bayan nakuda kwana biyu. Yaron yazo ba rai har ya fara rubewa.
Na biyun kuma tiyata aka mata bayan tasha nakuda wuni da kwana amma yaron ya koma bayan awa biyu.
Lokacin sallama likitan ya bada shawarin kar ta fara nakuda in ta sami wani cikin, ayi tiyata a cire yaron yana cika wata tara.
Sun karbi shawarin hannu bibbiyu amma sai aka sami akasi ranan da ya kamata suzo mai gidan yayi tafiya kuma wayarsa bata shiga.
Sirikarta tayi murna da hakan don a tinaninta asara za'a daurawa danta don wancan lokacin ma sai da ya saida rikekken bujuminsa.
An kira unguzoma tayi fama har ma tasa mata kwayan nakuda ta kuma daura ruwan karfin nakuda. Shi ya jawo fashewan ma'haifa haka aka debota rangai rangai.
A karshe dai an samu ceton ranta.
Sai dai:
Shekarunta 20.
Ba yaro.
Ba ma'haifa.
Ba daman sake haifuwa.
Bayan ta farfado yanzu muna tinanin wane irin bayani zamu mata ta gamsu.
Idan akwai shawari mu hadu a comment section.
Naku Dr Abdulkadir Musa Abba

01/10/2025

Gwamna Abba Kabir ya zargi kwamishinan da janye jami'an ƴansanda daga filin taro na Sani Abacha yayin da ake dab da fara bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ƴancin kai.

Karin bayani - https://bbc.in/4nAjKZG

01/10/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Kano ta dakatar da Malam Lawan Triumph daga yon wa'azi

Majalisar Shura da gwamnatin Kano ta kafa ya sanar da dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa'azi.

A wani taron manema labarai da Sakataren majalisar, Alhaji Shehu Wada Sagagi ya yi a yau Laraba, ya ce an dakatar da Malam Lawan ne domin bashi damar ya zo gaban majalisar ya kare kan sa daga zarge-zargen da ake yi masa na yin kalaman ɓatanci ga Ma'aiki.

A cewar Sagagi, an dakatar da Malam Lawan har sai an kammala bincike da jin ta bakin sa a matakin Majalisar ta shura.

Ya kuma yi kira ga ƴan siyasa da su guji tsoma baki a batun, inda ya bukaci da a kyale kwamitin ya kammala aikin sa.

Sagagi ya tabbatar da cewa Majalisar za ta yi aiki tsakani da Allah ba tare da don rai ko rashin adalci ba.
Daga Jaridar Daily Nigeria

Want your organization to be the top-listed Non Profit Organization in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address


260, Sani Mainagge
Kano