Sir Wisdom II
Ba ma gina fahimta a kan hasashe; muna jingina bincikenmu ga ilimin kimiyya da tarihin da ake da shi.👌👌
17/06/2026
A shekarar 2022, wani babban jirgin ɗaukar kaya mai suna Felicity Ace, ya nutse a zurfin tekun Atlantika, tare da motoci kusan 4,000 na alfarma, ciki har da Porsche, Bentley, Audi, da Lamborghini waɗanda jimillar darajarsu ta kai sama da dala miliyan 400.
Jirgin yana kan tafiya daga Jamus zuwa Amurka lokacin da wuta ta tashi yana tsakiyar tafiya, kusa da tsibirin Azores.
An ceto duka ma’aikatan jirgin, amma wutar ta bazu da sauri, kuma bayan kwanaki ana ƙoƙarin kashe ta, jirgin ya nutse a ranar 1 ga Maris, 2022.
A cikin jirgin akwai wasu daga cikin motoci mafi tsada a duniya, har ma da Lamborghini Aventador, wanda yanzu haka suna ƙasan teku har abada.
Masana suna zargin cewa batir ɗin lithium-ion ne s**a fara tada wutar, sai dai bincike har yanzu bai tabbatar da ainihin dalilin faruwar gobarar ba.
Abin da aka ɗauka a matsayin tafiyar kasuwanci ta al’ada,
ta zama ɗaya daga cikin mummunan hasara mafi tsada a tarihin duniya.
16/06/2026
SABON ANGO A DAREN FARKO!
Wata rana wani sabon Ango yana zumuɗin zai yi daren farko da Amarya, kwatsam saiga wani yana ƙwanƙwasa musu ƙofar gida, angon ranshi a ɓace yaje ya duba domin yaga waye ke buga musu ƙofar gida, fitar shi keda wuya sai yayi karo da wani bawan Allah kafin mutumin ya buɗe baki yayi magana, sai mai gida cikin fushi da ɗaga murya yace dashi "Mallam ko lafiya kuwa kazo kana buga mana gida da wannan daren?!
Mutumin cikin yanayin damuwa yace: "Wallahi yunwa nakeji don Allah ku taimaka mini da abinci" Cikin ɓacin rai wannan angon ya zazzage shi tare da korarsa ya hana shi abincin.
Tsabar jahilci da fushi irin nashi, sai ya dawo cikin gidan ya ɗauki hular shi ya bar gidan shi ga ran shi ya ɓaci, bayan wannan fitar da yayi wata da watanni, shekara da shekaru bai dawo ba, matar sai ta nemi alƙali ya raba musu auren...✂️
Allah buwayi gagara misala:
Bayan an raba auren bada jimawa ba tayi wani sabon auren, Ranar daren amarcin ta kuwa, sai wani abu ya sake faruwa mak**ancin abinda ya faru shekaru baya: wani mutum yazo yana buga musu ƙofar gida, Angon yace da ita taje ta duba waye ne a ƙofar gidan, fitar ta keda wuya kawai sai angon yaji ta fashe da kuka 😭😭.
sai ya biyota tare da tambayar ta "Yaya meye ke faruwa ko lafiya?". Sai tace dashi: "wannan mutumin ta nuna wanda ke tsaye a kofar gidan nasu shine angona na farko dana baka labari ya kori wani mai jin yunwa da yazo gidan mu neman abinci" Tana rufe baki sai sabon mijin nata ya fashe da kuka yace da ita: "Toh wallahi bawani bane ya kora nine nan".
ALLAH kenan😢😢😢...
Yan'uwa abinda bamu so ayi mana kada muyi ga wasu domin ita rayuwa bata da tabbas domin wanda ka cutar yau gobe zai iya zama silar taimakon ka
Allah yasa mu wanye lapia☺️
Sir Wisdom II pen 🖊️🖊️
09/06/2026
A ranar 13 ga Nuwamba, 2008, Dallas Wiens, wani ma’aikacin gine-gine daga Texas, ya samu mummunan rauni a fuskarsa bayan ya taɓa wayar lantarki mai ƙarfin wuta sosai. Wutar ta ƙone shi har fuskar sa ta narke gaba ɗaya.
An garzaya da shi zuwa Parkland Memorial Hospital a Dallas, inda likitoci s**a fara aikin ceto rayuwarsa cikin gaggawa.
A matakin farko, dole ne su cire dukkan fata da nama da wuta ta lalata, har da cire idonsa na hagu (enucleation) Idonsa na dama kuwa yaji rauni sosai, an kare idon da wani ɓawon fata da aka rufe shi da shi.
A watanni da s**a biyo baya, Wiens ya sha manyan tiyata da dama, A wata babbar tiyata, likitoci sun yi aiki har na tsawon awa 36 cikin kwanaki biyu, suna amfani da tsokar dake gadon bayansa domin gina sabon tsarin fuskarsa.
Bayan wannan aikin, ya rage saura rabin fatar kansa kawai, sai ƙaramin nama a gefen hagu na haɓarsa, babu gira, babu idanuwan sa guda, babu hanci, kuma babu leɓɓa.🥹
Bakinsa ya rage k**ar wani siririn rami, yayin da idonsa na dama ya ci gaba da kasancewa ƙarƙashin rufin fatar da akyi masa saboda raunin da idon yaji.
Duk da dukkan ƙoƙarin da aka yi, Wiens ya makance har abada, kuma ya rasa yawancin siffar fuskar sa.
Daga baya an saka masa idanu na roba (ocular prosthesis) a ramin idonsa na dama.
A watan Maris 2011, ƙungiyar likitoci fiye da 30, da kuma ƙarin wasu likitoci 8, sunyi nasarar yi masa cikakken sauya fuska (full face transplant) a asibitin (Brigham and Women's Hospital a Boston)
Aikin ya ɗauki tsawon awa 15, kuma akayi yi nasarar mayar masa da sabuwar fuska, sai dai da wannan sabuwar fuska bata nufin an a iya dawo da ganinsa.
©️ Sir Wisdom II pen ... 🖊️
Click here to claim your Sponsored Listing.