Da,irar bunkure
DA'IRAR BUNKURE JAHAR KANO
AN BUDE WANNAN PAGE DAN ISAR DA SAKON HARKAR MUSULUNCHI KARKASHI MZAKZAKY
04/06/2023
11/02/2023
ADDINAN MUSLUNCI MUKE KIRA A KAI BA MAZHABA BA
— Sheikh Ibraheem Zakzaky a cikin Jawabinsa na tunawa da shekaru 44 da kafuwar Daular Musulunci a Iran.
"Mutanen da suke cewa wai abin da ya faru a Iran wai bazai yiwu ya faru a nan ba, su daina wannan tunanin wannan ba gaskiya bane. Abin da ya faru a Iran zai iya faruwa a ko ina in Allah ya so, nasan akwai wani lokaci da wayansu mutane s**a je s**a ziyarci Sayyid Khamene'i sai yake ce musu 'Wannan juyi da ya faru a Iran wannan kawai yin Allah ne' yace in Allah Ta'ala ya so yayi shi a Italiya za a yi shi a Italiyan. Allah Ta'ala al'amarinsa kumfa ya kun ne, in yaso ya tabbatar da Addinin nan a duk inda ya ga dama zai iya tabbatuwa da kuma wanda ya ga dama da kuma wanda ya ga dama."
"Kun ga Allah Ta'ala da ya aiko wannan Manzo a tsakankanin mutanen da suke bautan gumaka kuma suke ganin cewa abin mamaki ne ma ace Ubangiji ɗaya ne, sune Allah Ta'ala ya maida s**a zama wayannan masu busassun zuƙatan nan (Masu kwana da takobi tsirara) kullum ana ta faɗace-faɗacen ƙabilanci, to sune Allah Ta'ala ya tausasa zuƙatansu ya maishe su taurari wanda s**a karbi addinin nan s**a yaɗa shi a Duniya. To wannan Allah zai iya irin wannan a wannan muhalli. Ina ga nan wanda yake da tsohon tarihin kafuwar Addini, sai wasu s**e to ai ƙasar ba ta musulmi ne ai su kaɗai ba, to ai ko a Iran ɗin ma ba ta musulmi ne su kaɗai ba kuma ba ta Shi'a ko Sunnah ba (Dama su kan ce mana wai Shi'a) wai ai duk ba kowa ne Shi'a ba, sai muce to ku kuke wannan maganar."
"Addinan Muslunci muka ce muku ba Mazhaba ba, ba ana kiran Mazhaba ne ba, ana kira ga addinin Musulunci ne. Shi addinin Musulunci na kowa da kowa ne har na wanda yake ba Musulmi bane, shi wanda yake ba Musulmi ba in Addinin Musulunci ya kafu yana da 'yancin yayi addininsa, amma dai addinin Musulunci shine ke sama saboda shi yana da dokoki tsararru, kuma dokokin nan a tuna ba Mutum ne yayi ba Allah Ta'ala yayi dokokin (Ba mutum ne yayi ba). Ba tsarin mutum bane ko ganin daman mutum (Yin Alla
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the public figure
Telephone
Website
Address
Opening Hours
| Monday | 09:00 - 17:00 |