View Point Hausa

View Point Hausa

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from View Point Hausa, Media, .

27/05/2026

Barkanku da Sallah
Allah Ya Maimaita Mana

21/05/2026

HANYOYI UKU DA ZA’ABI ABI A DAKILE FADAN DABA A JIHAR KANO.
SHEIKH IBRAHIM KHALIL
VIEW POINT HAUSA

21/05/2026

Shugabannin Arewa Su Tashi Tsaye Domin Ceto Yankin — Janar Ibrahim Badamasi Babangida

Tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya yi kira ga shugabannin Arewa da su tashi tsaye domin ceto yankin daga mawuyacin halin da yake ciki, yana mai bayyana damuwarsa kan matsalolin tsaro, talauci da rashin ci gaba da s**a addabi yankin.

Janar Babangida ya bayyana hakan ne yayin da yake nuna damuwa kan yadda Arewa ke cigaba da fuskantar ƙalubale iri-iri da s**a haɗa da rashin tsaro, rashin aikin yi da kuma koma bayan ilimi da tattalin arziki.

A cewarsa, lokaci ya yi da shugabanni da masu ruwa da tsaki za su haɗa kai domin nemo hanyoyin da za su fitar da yankin daga halin da yake ciki kafin lamarin ya ƙara taɓarɓarewa.

“Shugabannin Arewa kuyi ƙoƙarin fidda yankin Arewa daga mawuyacin halin da yake ciki. Mu tamu ta kare. Ina ji a jikina kamar bazan tsallake wannan shekarar ba,” inji Janar Babangida.

Tsohon shugaban ƙasar ya jaddada cewa makomar Arewa tana hannun shugabanninta da matasa, yana mai kira ga al’umma da su rungumi haɗin kai, zaman lafiya da kuma jajircewa wajen cigaban yankin.

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan hanyoyin da za a magance matsalolin da s**a dabaibaye yankin Arewa da ma ƙasar baki ɗaya.

View Point Hausa

Website