Rasulul A'azam Foundation-RAAF
RAAF is the largest registered Shi’a organization in Nigeria.
16/05/2026
ALLAH YANA GANI..
Ayatullahi Bahjati (RA) yana daga cikin Manyan Malaman Hauza Musamman a ɓangaran "Aklaƙ" wanda yake da Numfashi mai tsarki so sai, zantukansa yake ratsa zuciya, mutane suke tasowa daga Tehran zuwa Qom domin su samu Sallar jam'i a bayansa da sauran karamomi masu tarin yawa da yake dasu.
Wata rana zaiyi lecture ga Daliban Ilimi akan tarbiyyar Ruhi da kuma faɗakarwa kamar yadda ya saba, Ɗalibai sun taru kunnuwa suna jiran gwala-gwalan kalamanda zasu fito daga bakinsa, kowa yana shaukin ya bude baki yayi magana, bayan yayi bismillahi yayiwa Annabin Rahama da Ahlinsa tsarkaka Salati shine yace:
أَلَمْ يَعْلَم بِأَنَّ اللَّهَ يَرَىٰ
Shin Ɗan Adam bai san cewa tabbas Allah yana kallon sa bane?!
Ayatullahi Bahjati (RA) yace: an gama Karatun yau, kowa ya saka wannan ayar a zuciyarsa abinda zai faɗa da abinda zai rubuta da inda zaije da abinda zai gani da sauransu ya sani Allah yana gani kuma shine mafi iya Hukunci masu Hukunci, wassalamu alaikum.
16/05/2026
BABBAR MAGANA.....
Na shekara sama da 50 ina karatu Kuma ina karantarwa, san nan bakin gwar gwado na karanta nassosi tun daga Ƙur'ani zuwa Hadisan Ma'asumai (as) gaba dayan wannan shekarunda nayi na samu Natija kamar haka:
Mutum yayi kokari gurin aikata dukkan wajibai, haka ya nisanci dukkan aikin Haramun, a mai makon aikin Mustahabbi to ka Shagaltu da Hidimtawa Al'umma, ranar Ƙiyama idan Allah ya tambaye ka, kace: Ayatullah Lankarani ne ya fadi.
03/05/2026
Kai tsaye daga wajen saukar Alqur'ani mai girma a garin Godiya ƙaramar hukumar Kabo ta Jihar Kano.
Sheikh Saleh Muhammad Sani Zaria (ha) da
Sheikh Bashir Lawal Kano (h)
Tare da shugabannin Rasulul A'azam (sawa)
S**a halatta tare da rakiyar dalibai yan Majmu'a
Duka a karkashin jagorancin Maulana Hujjatul Islam Wal Muslimin Sheikh Muhammad Nur Dass (h).
25/04/2026
An yi bikin aure mai ban sha’awa duk da halin yaƙi! ✌️🇵🇸💍
Duk da wahalhalun yaƙin da aka sha na tsawon lokaci, a yau an shaida wani abin alfahari a tsakiyar Gaza Strip, musamman a Deir al-Balah. An shirya wani babban bikin aure na haɗin gwiwa mai suna “Tufafin Farin Ciki 2”, inda ma’aurata 300 s**a daura aure tare! ✨❤️
An gudanar da bikin ne kusa da Al-Aqsa Hospital, tare da tallafin United Arab Emirates da kuma Khalifa bin Zayed Al Nahyan Foundation, a karkashin wani shiri mai suna “Gallant Knight 3”.
Wannan lamari ya nuna cewa al’ummar Falasɗinu ba su yarda da karyewa ba; duk da ƙalubale, suna ci gaba da son rayuwa da kuma riƙe ƙasarsu. Farin cikin nan wata shaida ce ta juriyarsu da ƙin mika wuya. 💪🏝️
Ahlulbaiti.com
12/04/2026
Majlisin Arba'in din Shahid Sayyid Ali Al-kamna'i rahamatullahi ta'ala alaihi Wanda aka gabatar yau Lahadi 12/04/2026 a Hussainiyyar Rasulul A'azam (sawa) dake Danbare Kano.
Karkashin jagorancin Maulana Hujjatul Islam Wal Musulmin Sheikh Muhammad Nur Dass (h)
Wakilan Shari'a Na Ayatullahil Uzma Sayyid Ali Al-kamna'i rahamatullahi ta'ala alaihi a Nijeriya.
03/04/2026
Ziyarar barka da salla da dalibai yan majmu'a s**a kai wa jagororin Mu'assasar Rasulul A'azam (sawa) ranar Laraba 02-04-2026. Kamar aka saba duk shekara bayan dawowarsu daga guraren tabligh.
A Hussainiyyar Rasulul A'azam (sawa) dake Hauzatu Baqirul Ulum (a.s) Danbare Kano.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the place of worship
Website
Address
Danbare Layout, Opp Bayero University New Site, Gwarzo Road
Kano