Napson Computer and Internet Cafe, Rimin gado
Is a business center and internet cafe. Here are our services. TYPING, PRINTING, ONLINE REGISTRATION
Wani Karin Haske Game Da Dibar Sabbin Ma'aikatan Shirin N-POWER BATCH C 2020
Muna samun tambayoyi game da shin me shaidar kwalin SSCE zai iya cikewa?
Ga yadda tsarin N-power yake :
1- N-power Agro
2- N-power Tax
3- N-power Build
4- N-power Health
5- N-power Teach
1- N-power Agro:
1- N-power Agro:
Wannan tsarin ana bukatar masu shaidar kwalin Diploma, HND da Degree, kuma wanda s**a karanci fandin Agric ko Nutrition.
2- N-power Tax
Wannan tsarin suna bukatar masu shaidar kwalin HND da Degree ne kaɗai, Kuma wanda s**a karanci fannin Finance, Economic, ko Accounting.
3- N-power Build
Wannan tsarin suna buƙatar masu shaidar karatun SSCE, Diploma, HND da Degree, bugu da kari wanda bashi da takardan shaidar karatu ma zai iya cikewa.
4- N-power Health
Wannan tsarin suna bukatar masu shaidar kwalin Certificate, Diploma, HND da Degree.
Daga cikin wadanda suke bukata akwai:
- Midwives
- Nursing
- Medical Record
- CHO, CHEW, JCHEW
- PHARMACY
- Biology
- Biochemistry
- Health education
- EHO, EVT, EHA
5- N-power Teach
Wannan tsarin suna bukatar masu kwalin NCE, Diploma, HND, da degree.
Kada ku manta ranan Juma'a(26/6/2020) mai zuwa za'a bude wannan Portal din Kuma portal address nasu bai canza ba, wanda
akai amfani da shi na baya shi za'ayi amfani (portal.npower.gov.ng)
Allah Ubangiji Ya bawa kowa sa'a.
Karanta abubuwan da ake bukatar wanda zai cika aikin N-power na rukunin C
Za a fara cike neman aikin a ranar Jumu'a 26 Jun
Daga, Ibrahiim M Bawa
Ma'aikatar Jin Kai da Kare Afkuwar Bala'o'i a Nijeriya da shirin tallafawa matasan Nijeriya na N-power ke karkashin ma'aikatar ta bayyana cewa za a fara daukar sabbin ma'aikatan shirin N-power na rukunin C a ranar Jumu'a mai zuwa 26 Jun 2020.
Ana bukatar wadanda s**a kammala sakandare har zuwa digiri na daya, dake bukatar neman aikin su tanadi wadannan abubuwan;
1, Suna Name ( Sunan Mahaifi ne farko 'Surname first)
2, E-mail
3, Password
4, Educational Background
5, National Youth Service Certificate
6, Birth Certificate
7, Local Government Identification letter
8, Bank Verification Number
9, Phone Number
10, Bank Account Number
11, Bank name
12, State origin, LGA, Community
13, Residential Address
14, State of Residence
15, Local Government of Residence
16, The program you prefer
Abin lura mai digiri ko HND ne kadai za su je takardar kammala bautar kasa da aka sanya a lamba ta 5 a wannan rubutun.
Masu takardun kammala;
SSCE,
ND
NCE
JCHEW
SCHEW
HND
DEGREE
Sune kadai za su iya neman aikin, masu takardu a hannu, ma'ana wadanda s**a kammala gaba daya har s**a amshi sakamakon jarabawarsu.
A tura ko'ina don sauran yan uwa su gani su amfana, kar a bar mu a baya wannan karon.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kano
701102