Ibrahim Gamji

Ibrahim Gamji

Share

Bahaushe / Activiste Hausa
جماعة أحباب رسول sufi/صوفي
cosmologist

If you see a tribalist in me, you are no doubt seeing a reflection of you in me.

09/06/2026

"ya ya sunan macen kunkuru da hausa?" Kunkuru na daya daga cikin dabbobi mafiya tsawon rai a duniya. Masana sun ce yana kai har fiye da shekara dari biyu. A raye.

Sannan ku sani akwai na tudu sannan akwai na ruwa. Kmr dai kwadi.

Kuma Nasan wani zai tunanin shin za a iya cire wannan kokon bayan nasa? Sam ba zai yiwu ba.

Kokom bayansa Wani ƙashi ne wanda yake hade da gangar jikinsa yana da Jijiyoyi, har cikin jikinsa.

Yana amfani dashi wajen kare kansa. Kuma Idan aka matsa masa ta ƙarfi ko aka buge shi, yana iya jin zafi kamar yadda mutane ke ji Idan aka buge Su Akan ƙashi.

Sannan yanada Jini da ke zagayawa ta ciki. Shi ya sa idan da zai samu rauni ko ya tsage, zai zubar da jini kamar dai sauran sassan jikinsa.

Sannan Masan sunce Kunkuru na daga cikin dabbobin da s**a fi juriyar yunwa da ƙishirwa a duniya.

Wasu daga ciki s**an kan jure har watanni ba tare da cin wani abu ba idan yanayi yayi tsanani.

Macen Kunkuru tana yin ƙwai ne. ba wai haihuwar jarirai kai tsaye ba.

takan tona rami a cikin ƙasa kamr yanda kadangare yakeyi sannan ta ajiye ƙwan.

Tana yin kwai har zuwa 30.
Bayan ta gama, se ta rufe ramin ta bar ƙwai din a cikin Ramin Har ya isa kyankyashe kansa da kansa ba Wai uwar ce take kyankyashe Kwan dakantaba.

Kuma Jariran kunkuru da zarar sun kyankyashe kansu.kai tsaye suke fara tafiya su shiga ruwa ko daji, ba uwarsu bace ke rainon su.

Sannan masana sun ce wani nau'in kunkurun na haihuwa sau ɗaya a shekara.
Wasu sau uku (3).

Sai dai duk da cewa kukuru na yin kwai da yawa ammaa bayan sun kyankyashe kan su sanadiyyar rashin kulawar uwa kadanne ke tsira.

Ga tamabaya ya ya sunan macen kunkuru da hausa?

Ibrahim Gamji

08/06/2026

Na daina bautar ƙungiyar addini tun tuni. Da ni ɗan ganin kashinin batijjane ne, ba kowa ni ke gani a matsayin musulm ba, musamman ma Shi’a. Kallon gara arna nike musu. In har malami ba batijjani ba ne, ko me zai fada ba zan saurara ba. Idan aka ce batijjanen malami ya yi kuskure, to ba zan taɓa yarda ya yi ba.

Daga baya na fara confusing, na fara judging ƙafatan tijjaniyawa da ayyukan wasu, na rika kallonsu a matsayin mushrikai. Sai kawai na canza na koma Salafi.

Na saba da abubuwa ba tare da tsattsauran ra’ayi ba. Na saba da girmama duk wani abu da ya shafi Ma’iki. Ina yarda da hadisai kowane iri, sai kawai na ji ƙwalkwale-kwalkwalenn abubuwan da kaina da zuciyata ba za ta iya ɗauka ba. Na fice na yi kundun bala na koma Imamiyya Shi’a, ba Rafidi ba. Can kau ko zama, ban yi ba, na yi fitar burtu.

Daga baya na yi tunanin kodai in zama sectless tun da kowanne yana da ra’ayinsa da ban yarda da shi ba, ko kuma in buɗe sabuwar Darika tawa ta kaina, in ɗauki hayar muridai kafin samun permanent.🤨

A Tijjaniyyance, ban yarda da wasu tatsuniyoyi ba, da wasu karamomin da s**a wuce misali. Amma ina girmama bayin Allah.

A Salafance, ban yarda da tsattsauran ra’ayin addini ba. Daga Alƙur’ani sai hadisai mutawatir na yarda 100%, amma hadisi Ahad wani lokaci ni kan zaɓi “Mashhur” ko “Aziz” kawai dai Ina zaɓar wanda bai ci karo da Alƙur’ani ba, kuma yake koyar da ilimin zamantakewa ko zaman lafiya. Amma ba na yarda da wanda ke koyar da tsattsauran ra’ayi ba.

A Shi’ance, ba na da wani hadi da su wanda ya wuce su masoya Ahlul Baiti ne. Kuma ba za mu bar masu ƙaunar Ahlul Baitin su kadai ba. Mutum ya daɗe bai kirana danShi’a ba in har don faɗar falalar iyalan Annabi ne. Ina girmama Khulafā’ur Rāshidīn dukkansu, muna son matan Manzon Allah dukkansu.

Na ga kowanne ina da jibi da su, na rasa matsaya. Sai kawai na duba na ga wani malami na fi so… sai ga Sheikh Burhan al-Khaulahi ne… Daga nan kawai na koma Sufi ɗan kan katanga.

A yanzu musulmi a wajena shi ne wanda ya ce shi musulmi ne, bana bukatar amincewar wasu akai.

Kuma kasancewar mutun mutumin kirki wanda bai cutar da kowa wanda ke alfanar al'umma shi ne mafi mahimmanci a wajena fiye da kasancewarsar dan akidara ko addini na, ka daɗe ba ka buɗe sabuwar ƙungiyar addini ba, kai ka daɗe ma ba ka buɗe sabon addini ba... kai ta shafa.

Ibrahim Gamji

07/06/2026

Jama'a ko ina labarin

Asadud-Bandits?

07/06/2026

"The government should seized the guns of the local people. After that, Fulani bandits tricked them by collecting their rifles in exchange for cows, or machine guns in exchange for herds of cattle (hundreds )and sometimes even cars or houses" "~Gumi~

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address

Kano