DZ ABUL
teaching
21/06/2025
ππππππ ππ πππππππ ππππππ πππππππππ ππππππ πππππππππ πππ
Siradul MustaΖim (hanya madaidaiciya) wanda aka faΙa cikin suratu Fatiha shine: Komawa zuwa ga Zatin Allah da komawa cikin Soyayyar Manzon Allah SAW, da kuma BAQAβI tare da zatin Allah Da Narkewa cikin Zatin Allah (batare da Hululi da Ittihaadi ba domin Allah ya tsarkaka ya sauka ko ya haΙu da jikin Abun Halitta) da Narkewa cikin Soyayyar Manzon Allah SAW, Da Neman Sanin Allah (Maβarifah) ta hanyar Shi da Siffofinsa da Sunayensa. Da Tabbatuwa akan Bin Sunnar Manzon Allah SAW.
Duk wanda ya dawwama akan haka a duniya toh ya tabbatar zai Samu Istiqaama, wanda kuma bai dawwama akan Haka ba toh bazai samu ba, duk lokacin da istiqaamarka ta ragu a rayuwar duniya toh zaka haΙu da tawaya a gobe Ζiyama.
Ku komar da ZuΖatanku zuwa ga Allah, ku rayar da lokutanku da neman kusanci ga Allah da Ιebe kewa dashi da soyayyar Manzon Allah SAW, Ku Sani Rayuwar nan TaΖaitacciya ce Kuma Gashi abun nema acikinta suna da yawa.
Ku tashi kuyi ΖoΖari a duniyar nan idan mutum Ya mutu ba zai samu damar furta LA ILAHA ILLALLAHU kafa Ιaya tak ba. Duniya wajen Aiki (Ibaadah) ne babu Hisabi Lahira kuma wajen Hisabi ne Babu Aiki.
Allah Ya Tabbatar da duga-duganmu akan SiraΙil Mustqeem.
Β©οΈAliyu Uthman Bashir
γviralγ·
19/06/2025
TAFAKKURI
tabbas rijalu sun san cewa wannan yakin da ake a isra'il dama sun san zaizo.
domin ba arokon allah abu yaki bayarwa,mutane sunyi addu'o'i akan zaluncin isra'il ga falastinu,suna masu rokon allah da ismul azim,suna jefawa a ramzi akan allah ya ruguzasu,
tabbas yauko gashi ismul'azim (makami mai linzami) sai sauka suke suna ruguza garin.
muna godema allah dawannan ni'ima da tasauka abirnin muslunci, tabbas wannan nasarace ga musulmin duniya.
makami mai linzami, akwai wani sirri acikinsa inkai taffakkuri sosai, domin wani (alifi) ne wani (hakuri)ne.
amma nabauwa masana asrarai suyi bayani akai, muna tuba
allah ya karamana son shugaba s a w da shehu tijjani rta da shehu ibrahim inyasss rta
10/06/2025
BAYANI AKAN WUSULI DA KOFAR MA'ARIFA
WUSULI shine saduwa acikin wani abu a harshen hausa kenan.
wusuli a sufanci shine bawa yayi fana'i (yakare) acikin halarar allah, yazama baya ganin wanin allah sai allah, shine fadin hadisinnan (kanallahu wala shai'a ma'ahu) idan bawa yai haka ya shiga cikin wannan hali to shine akecewa yashiga cikin jazba (maye na fana'i).
yadda ko bawa zai shiga wanna hali shine idan shehinsa zai mai tarbiyya zai bashi zikirai Kamar haka:
salatil fatihi 500 sau uku
al'auwalu..........al'badinu 500 sau 5
mu'auwali. kafa 3 sau biyar
sai taffakkuri. da sauransu.
domin kowane shehi da yadda yake tarbiyyar muridansa.
to bayan yazo ammai imtihani za agane yayi wusuli kokuwa dai, ya danganci kyan ruhin murudin, idan yayi zai bayanin abinda yagani kamar na farko........ na karshe, wato fana'i(wusuli) shine kamar Tashar garin ma'arifa.
wanan shine ake kira da wusuli atakaice,
na daddatse wasu abubuwan sabida aikin sirrine.
KOFAR MA'ARIFA
shine idan murudi yayi wusuli yasamu fatahin farko na fana'i, sai abashi (sirrin fatiha) da (salatul fati )da (sirrin ziyara) da (sakirtu ) ya nemo sunaye guda dai-dai acikin kowannansu,wannan sunaye guda 4, sune kofa, kowace hadara akwai sunanta da zai dinga shaida aikinta a musha'hada dashi.
wannan shine kofar ma'rifa.
muna rokon allah ya karomana faida bijahi shehu barhama abdullahi inyass rta
Click here to claim your Sponsored Listing.
Contact the business
Telephone
Website
Address
Kano