Hamza
Gaskia Jarin Dan Adam
12/05/2026
Eugene Daniel Bakar Fata Dan Shekaru 16 Da Aka Rataye Saboda Tsorata Yarinya Farar Fata 'Yar Shekara 16
A watan Satumba na shekarar 1921, a ƙaramin garin Pittsboro da ke gundumar Chatham cikin jihar North Carolina a kasar Amurka, Eugene Daniel, ɗan shekara 16, ya zama wanda aka zalunta, kuma ɗaya daga cikin munanan ayyukan cin zarafin bil'adama saboda bambancin launin fata na zamanin Jim Crow. Abin da ya fara k**ar wasa ya ƙare da wani babban bala'i.
Eugene Daniel wani yaro bakar fata ɗan shekara 16, wanda ke zaune tare da iyayensa a kusa da Pittsboro. A ranar 16 ga Satumba, 1921, mahaifinsa ya aike shi gidan maƙwabtansu, don ya aro masa igiya. Ya kwankwasa kofar gidan, amma shiru babu wanda ya amsa. Abinka da yaro sai ya jingina da ƙofar gidan, sai ƙofar ta buɗe, sai ya shiga ciki, yana Excuse me don ganin ko akwai wanda ke gidan.
Duk da yake babu wani abu da ya aikata, amma ƙaramar 'yar mai gidan Gertrude ta firgita, wacce ke barci a ɗakin kwananta lokacin da ya shiga gidan na ɗan lokaci. Cikin tsoro, ta fita daga ɗakin. Da ya fahimci yadda za a iya yiwa lamarin mummunar fahimta, Eugene ya gudu ya bar gidan cikin sauri ya koma gida.
Tsoron da yarinyar ta ji ya jawo hankalin manya a gidan cikin sauri, kuma a cikin yanayin wariyar launin fata na lokacin, an mayar da abinda ya faru mai tsanani fiye da yadda yake a zahiri. Mutane sun yaɗa labarin cewa wani matashi Baƙar fata ya shiga ɗakin kwanan wata yarinya farar fata, saboda tsauraran ƙa'idodi da rashin adalci na zamantakewa na Jim Crow South, an ɗauke shi a matsayin barazana duk da cewa bai yi wani laifi ba.
Washegari, 'yan sanda sun yi amfani da karnukan bin diddigin Daniel, s**a k**ashi su ka kai shi gidan yarin gundumar Chatham da ke Pittsboro. Maimakon kare shi ko binciken lamarin, yan sandan sun zama sababin abinda ya biyo baya.
A daren nan, wasu fararen fata kusan hamsin s**a taru a wajen gidan yarin, s**a k**a Daniel s**a tilasta masa shiga mota. Ƴan daban turawan sun yi tafiya mai nisa da shi daga gabashin garin zuwa wani yanki kusa da wata gada a tsohuwar hanyar Raleigh. A can, cikin duhun daren ranar 18 ga Satumba, gungun turawan su ka rataye Daniel da sarka kuma s**a rinka harbinsa akai-akai.
Gawar da aka rataye ta zama abin kallo ga al'ummar yankin. Mazauna yankin fararen fata sun ɗauke ta a matsayin abin jan hankali ga jama'a, ba tare da nuna girmamawa ga Daniel a matsayin ɗan adam ba. Mutane suna zuwa daga wurare daban-daban don kawai su ga gawarsa da aka rataye suyi dariya.
Zuwa ranar Litinin, 19 ga Satumba, 1921, kimanin mutane 1,000 ne s**a yi tattaki zuwa wurin don ganin gawarsa kafin a sauke ta. Maƙwabtan wajen da jami'an yankin duk sun halarci wajen, wanda ya nuna yadda ta'addancin launin fata ya zama ruwan dare a cikin al'umma.
Shekaru da yawa, labarin Eugene Daniel ya ɓace daga tunanin jama'a, an manta da shi kuma wasu ma ba su san da shi ba. Cikakkun bayanai game da mutuwarsa da tashin hankalin da ya sha sun ɓace, an binne shi a ƙarƙashin yin shiru da sakaci.
Sai a shekarar 2021, ƙarni ɗaya bayan mutuwarsa, aka dawo da labarinsa. A bikin cika shekaru 100 da kisan gillar, Hukumar Kwamishinoni ta Gundumar Chatham ta fitar da takardar neman afuwa a hukumance kan gazawar gwamnati na kare shi, da kuma yadda shugabannin yankin s**a bar kisan ba tare da an hukunta kowa ba. Jami'ai sun fahimci cewa jami'an tsaro a wancan lokacin sun gaza wajen tabbatar da adalci ko bin doka da oda.
Ƙungiyoyin al'umma, zuri'a, da shugabannin jama'a sun yi aiki don tunawa da Daniel da sauran waɗanda aka yi wa ta'addancin bambancin launin fata a gundumar Chatham. An sanya alamun tarihi, kuma an nuna ƙasa da aka tattara daga wurin da akai ma sa kisan gilla a cikin nunin kayan tarihi na gida a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin fahimtar wannan tarihi mai raɗaɗi.
Click here to claim your Sponsored Listing.