Sani Shuaibu Suleman

Sani Shuaibu Suleman

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Sani Shuaibu Suleman, Public Figure, Kano.

01/12/2022

YABON MUTANE A KAN MAMACI

An kar6o daga Anas dan Maliki, Allah ya yarda da shi, ya ce: An wuce da gawa sai aka fadi alheri a gare ta, sai Manzon Allah SAW ya ce: " ta wajaba". Sai aka kara wuce wa da wata gawar, sai aka fadi Sharri a kanta, sai Manzon Allah SAW ya ce: "ta wajaba". Sai Umar bin Khattab RA ya ce: mece ce ta wajaba?' sai Manzon Allah SAW ya ce: " wanna kun fadi alheri a kanta , sai Aljannah ta wajaba a kanta, wannan kuma kun fadi sharri a kanta , sai wuta ta wajaba a kanta, ai Ku shaidun Allah ne a bayan masa!"

Bukhari ne ya ruwaito.

01/12/2022

Daga Abu Bakrah, Allah ya yarda da shi , daga Annabi Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: hakika zamani ya kewayo ya dawo kamar yadda yake ranar da Allah ya halicci sammai da kassai. ita shekara wata goma sha biyu ce , hudu daga cikin watannin masu alfarma ne. guda uku a Jere, sune: Dhul Qidah da Dhul Hijja da Muharram, sannan watan Rajab, watan Kabilar mudar Wanda ke tsakanin Jumada da Sha'aban.

Bukhari da Muslim ne s**a ruwaito shi.

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Kano