Inusawa Student Association
This page is for all students of YADAKUNYA WARD it involved both graduate, undergraduate and postgraduate
12/04/2025
*SANARWA DAGA KUNGIYAR DALIBAN YADAKUNYA*
Assalamu Alaikum 'yan uwa,
Muna so mu tunatar da ku game da cigaban da kungiyar mu ta Yadakunya Student Association ke yi domin tallafawa ilimi a cikin al’ummarmu.
Muna farin cikin sanar da ku cewa karatun extramural ya cigaba yau, kuma zai ci gaba da kasancewa kamar yadda aka saba a duk ranar *Juma’a* da *Lahadi* daga karfe 2:00 na rana zuwa 4:00 na yamma.
Wurin Karatu:
Makarantar Firamare ta Kingawa Nomadic, Inusawa
Layin Alh. Abdulrazaq Bello, cikin Islamiyyar Muhammad Bello
Muhimman bayanai:
Karatun kyauta ne.
Duk daliban SS suna da damar zuwa kuma muna maraba da su hannu bibbiyu.
Muna koyar da muhimman fannoni guda biyar na sashen kimiyya: Lissafi, Turanci, Physics, Chemistry, da Biology.
Muna rokon ku da ku taimaka wa kanku ta hanyar halartar wannan karatu domin cigaban rayuwarku da makomar ku.
Haka kuma, muna kan shirin gudanar da taron bita (seminar) kan muhimmancin ilimi da hanyoyin samun nasara a jarrabawa da shiga manyan makarantu.
Karin Bayani:
Ga wadanda za su zauna JAMB na bana, ana rokon su su zo a ranakun karatu domin karbar shawarwari da taimako na musamman.
Ko kai ba ka cikin makaranta amma kana bukatar ci gaba da karatu ko taimakon ilimi, muna maraba da kai sosai.
Mu hada kai mu gina makomar mu ta hanyar ilimi.
Signed YADAKUNYA STUDENTS ASSOCIATION
HELLO MEMBERS OF THIS ASSOCIATION. It has been a while hope you are all doing fine.
IFTAR MUBARAK IN ADVANCE
Contact the ASSOCIATION officials via:
FACEBOOK:INUSAWA STUDENT ASSOCIATION
WHATSAPP NO:07036336279
Please help us shere with our people to make it work...
Inusawa Student Association Send a message to learn more
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the university
Telephone
Address
Kano