GIST ARENA
Gist Arena shares love stories, travel experiences, and moments that connect people. Real journeys. Real emotions. Real people.
Terror!st uploads a video of a group of other band!ts just concluding their Salat al-Eid, the background is seen with multiple combatants, kids and their wives in the area.
21/03/2026
NAYI NADAMAR YIN SALLAR IDI A MASALLACIN KUNDILA, JIHAR KANO
A yau na gudanar da Sallar Idi a wani masallaci da ban tabbatar wanne nake bi ba, tsakanin Masjid Sahabah da Masjid Jami’ur Rahma dake unguwar Kundila a Jihar Kano. An gudanar da Sallar ne da misalin ƙarfe 08:00 na safe, a ranar Juma’a.
Abin da ya faru shi ne, duka masallatan guda biyu suna amfani da lasifika masu ƙarfi, ta yadda har zuwa Gadar Lado ana iya jin kowannensu. Haka kuma, limaman biyu sun karanta Suratul A’ala a raka’a ta farko da kuma Suratul Ghashiyah a raka’a ta biyu.
Wannan ya sa dole sai mutum ya yi matuƙar nutsuwa kafin ya gane wanne limami yake bi. Ni kaina da ƙyar, da ƙoƙari sosai, na samu na kammala Sallar tare da bin limami guda ɗaya.
Abin takaici, sakamakon wannan rikicewa tsakanin sautukan masallatan, sun sallame Sallar tasu ba tare da sun kammala yadda ya dace ba. Hakan ya jawo sun rasa Sallar Idi ta wannan shekarar.
Saboda haka, muna kira ga Hukumar Malamai (Council of Ulama) ta Jihar Kano da su zauna su tsara yadda za a samu bambancin lokaci tsakanin masallatai, domin kauce wa irin wannan matsala a nan gaba.
A kwanakin baya na ga rubutun Sunusi Danjuma Ali kan irin wannan matsala a Sallar Juma’a, kuma har yanzu ana ci gaba da samun irin wannan lamari na yin Sallah a lokaci guda.
Allah Ya ba mu ladan Sallar Idi da muka yi, Ya kuma sa ta zama karɓaɓɓiya.
Cx: Sanusi danjuma ali
Click here to claim your Sponsored Listing.