Hausa View

Hausa View

Share

Domin samun sahihan labarai na cikin gida da kuma ketare. Wannan shafin zai kuma rika tabo batutuwan da s**a shafi al'umma kai tsaye.

05/06/2026

Gwamnatin Najeriya na shirin dawo da sama da ’yan ƙasa 1,000 daga South Africa sakamakon karuwar rikice-rikicen ƙyamar baƙi a ƙasar, wadda ta daɗe tana karɓar ma’aikata daga sassan Afirka.

05/06/2026

Kamfanin Anthropic ya yi kira da a rage saurin ƙera manyan tsarin AI, inda ya ke gargadin cewa wasu sabbin nau’ikan AI na iya zama masu wahalar sarrafawa a nan gaba.

Mene ne ra'ayin ku?

05/06/2026

Babbar Kotun Kaduna dake Najeriya ta yi gwanjon wasu kadarorin tsohon ɗan majalisa, Mahmood Sani Sha’aban, kan wata takaddamar bashi da ta daɗe tana gudana.

05/06/2026

Liverpool na ƙara ƙoƙarin ɗaukar ɗan wasan Ivory Coast, Yan Diomande, amma RB Leipzig ba ta son sayar da shi.

Shin kuna ganin ya dace RB Leipzig ta siyar shi?

05/06/2026

Dan majalisar wakilai, Hon Bamilade Salam ya ce ana sakaci da matsalar tsaro a Nigeriya ne saboda bai shafi masu mulki da ýaýan su ba ne, talakawa ne kadai ke fama da radadin da hakan ke hai farwa.

Mene ne ra'ayin ku akan wannan batu?

04/06/2026

Shugaban fadar shugaban kasar Najeriya, Femi Gbajabiamila ya ce an samu ci gaba wajen kafa rundunar ‘yan sandan jihohi, kuma za a gabatar da gyaran kundin tsarin mulki nan ba da jimawa ba.

04/06/2026

Rukunin farko na Alhazan Jihar Kebbi a Najeriya, na Hajjin 2026 sun isa Birnin jihar, wanda hakan ya nuna fara dawo da alhazan jihar gida a hukumance.

Wani fata zakuyi musu?

04/06/2026

An kammala bikin cika shekaru 70 na Rundunar Sojin Ruwan Najeriya ƙarƙashin jagorancin Admiral Idi Abbas, tare da halartar manyan jami’ai da baƙi daga ƙasashen waje.

Wani fata zakuyi musu?

04/06/2026

Gwamnatin Nijeriya ta baiwa masu amfani da solar damar sayar da wutar da ta yi musu yawa ga kamfanonin raba lantarki.

Shin kuna ganin hakan ya dace?

04/06/2026

Ministan harkokin wajen Amurika, Marco Rubio yace kasar Amurka ta yi hadin gwiwa da Najeriya kan yaki da ta'addanci.

Mene ne ra'ayin ku?

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Address

Kano