DanMasani RADIO

DanMasani RADIO

Share

DANMASANI ONLINE GLOBAL RADIO. MUN SHIRYA TSAF DOMIN FADAKARWA, ILIMANTARWA DA KUMA NISHADANTARWA.

10/06/2026

Kungiyar ’Yankwangila Ta Jihar Katsina Ta Gudanar da Taron Shekara, Ta Yi Canji da Cike Gurabu na Shugabanni.

Daga Auwal Isah Musa| Katsina Times.

Kungiyar ’Yankwangila ta Jihar Katsina ta gudanar da taronta na shekara tare da shirya lakcar wayar da kai domin kara wa mambobinta ilimi da kwarewa, inda kuma ta amince da wasu sauye-sauye a tsarin shugabancinta ta hanyar nada sabbin jami’ai da sauya wa wasu mukamai a shiyyoyin Katsina, Daura da Funtua.

Tun farko da yake jawabi maraba a taron, Shugaban Kungiyar, Abdullahi Esha, ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin mataki na hada kan mambobi domin nazarin ci gaban kungiyar da kuma tattauna hanyoyin bunkasa ayyukanta.

Ya ce wannan ne karo na farko da aka samu halartar mambobi daga kusan dukkan sassan kungiyar, yana mai bayyana yadda kungiyar ta samu ci gaba tun daga kafuwarta.

“Mun samu gagarumar nasara a wannan tafiya. A lokacin da muka fara, mambobinmu ba su wuce mutum shida zuwa bakwai ba, amma a yau muna da tsakanin mambobi 280 zuwa 300,” in ji Esha.

Ya kara da cewa hadin kai da fahimtar juna da ke tsakanin mambobin kungiyar na daga cikin manyan nasarorin da s**a samu, yana mai jaddada muhimmancin ci gaba da gudanar da irin wadannan taruka domin musayar ra’ayoyi da shawarwari.

“Akwai bukatar mu ci gaba da haduwa domin tattauna matsalolin da ke gabanmu da kuma hanyoyin magance su. Wannan zai tabbatar da dorewar kungiyar har zuwa nan gaba, hatta bayan wadanda s**a assasa ta ba su nan,” ya bayyanar.

Daya daga cikin muhimman abubuwan da taron ya kunsa shi ne gabatar da lakca kan harkokin kwangila da hanyoyin inganta aiki, wadda Q.S. Faisal Ahmad ya gabatar. A cikin lakcar, Faisal, ya yi karin haske kan dabaru da ka’idojin gudanar da ayyukan kwangila, tare da bayyana muhimmancin kwarewa, gaskiya da bin ka’idoji wajen samun nasara a harkar.

Bugu da kari, taron ya kuma yi nazari kan ayyukan kungiyar na shekarar da ta gabata, inda aka tattauna nasarori da kalubalen da aka fuskanta tare da daukar matakan gyara domin kara inganta tafiyar kungiyar.

Sakataren kungiyar, Yakubu Maicanji, ya sanar da amincewa da wasu nade-nade da sauye-sauyen mukamai domin cike guraben da s**a samu gibi da kuma saukaka gudanar da ayyuka a shiyyoyin kungiyar.

Sabbin nade-naden sun hada da: Injiniya Lawal Yunusa daga Shiyyar Funtua, wanda aka nada a matsayin Auditor General, Murtala Shehu daga Shiyyar Daura, wanda aka nada Assistant Secretary, da kuma El-Salisu Kawauri, wanda aka nada Assistant PRO.

Maicanji ya bayyana cewa an yi wadannan gyare-gyare ne domin kusantar da shugabanci ga mambobi a yankuna daban-daban.

“Duba da yanayin da ake ciki yanzu, ba lallai ne a rika tado mutum daga nesa zuwa Katsina domin gudanar da wasu ayyuka na gaggawa ba. Wannan tsarin zai taimaka wajen magance jinkiri da kuma saukaka tafiyar da harkokin kungiyar,” in ji shi.

Taron ya karkare da zaman tattaunawa, bayar da shawarwari da karbar tsokaci daga mahalarta, inda aka jaddada bukatar kara hadin kai, bunkasa kwarewa da kuma samar da sabbin dabarun da za su taimaka wajen karfafa kungiyar da tabbatar da ci gabanta.

A karshe, mahalarta taron sun bayyana gamsuwarsu kan yadda aka gudanar da taron, tare da nuna fatan cewa matakan da aka dauka za su kara habaka ayyukan kungiyar da inganta rayuwar mambobinta.

10/06/2026

Deputy of the President of the Senate, Senator Barau I Jibrin, has urged universities and other tertiary institutions in the country to prioritise research and its commercialisation as done by higher institutions in developed nations.

10/06/2026

Kungiyar Izala..
Sheikh Abdullahi Bala Lau ke jagoranta ta tabbatar da cewa 'yan ta'adda sun kashe daga daga cikin shugabanninta a Kebbi Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bayyana cewa shugaban Izala na karamar hukumar Besse, Malam Yahaya Balli ya rasu a hannun masu garkuwa Shugaban Izala na kasa ya yi kira ga limamai da su dukufa da yin addu'a domin rokon Allah ya kawo karshen matsalolin tsaro da ake fama da su..

10/06/2026

Mai dakin Gwamnan Jihar Katsina Hajiya Fatima Dikko Radda, ta sha alwashin cigaba da yin bakin kokarin ta wurin taimakon mata da ke fama da lalurar cutar sankara(Cancer) a Jihar Katsina.

Hajiya Fatima Dikko Radda ta furta hakan ne a lokacin kaddamar da shirin kula da mata masu fama da lalurar cutar sankarar mama(Breast Cancer) a Katsina.

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Malam Faruk Lawal, shi ne ya kaddamar da shirin a farfajiyar Asibitin Janar Amadi Rimi da Ke Batagarawa.

Gidauniyar mai dakin Gwamnan wato Pledging Aid Charity Foundation (PAC-F) hadin Guiwa da Ma'aikatar Lafiya tare da Gidauniyar Revive Belgium daga Kasar Belgium ne ke daukar nauyin gudanar da shirin.

Da take magantawa a yayin kaddamar da shirin, mai dakin gwamnan ta bayyana cewa, shirin na daga cikin kokarin gidauniyar ta wurin tallafawa mata masu fama da lalurar.

Hajiya Fatima Dikko Radda ta jaddada bukatar da ke akwai ga mata akan su ziyarci asibitoci domin sanin matsayin su akan lalurar, domin saurin gano ta shi ne ke taimakawa wurin shawo kan ta.

Daga nan sai ta yaba wa Gwamna Dikko Umaru Radda akan yadda yake bata kwarin guiwa wurin gudanar da irin wadannan ayyukan jin kai ga mabukata.

Ta kuma yabawa likitocin da ke gudanar da shirin, da dukannin masu ruwa da tsaki da suke taimakawa domin ganin an samu nasarar gudanar da shirin.

Hausa Digital RTV ta tsinkayi wasu da s**a maganta a lokacin taron suna yabo da jinjina ga mai dakin Gwamnan Hajiya Fatima Dikko Radda, akan dumbin ayyukan jin kai da take aiwatarwa.

Daga bisani mai dakin Gwamnan tare da Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Malam Faruk Lawal, sun duba masu fama da lalurar da aka riga aka yi wa tiyata.

Want your business to be the top-listed Media Company in Katsina?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address

No. B27. Khalil Raman Shopping Complex. High Court Roundabout. Daura Road Katsina
Katsina
820221