Dandume FORUM
Mun bude shine don sada xumunta da nishadantarwa illimantarwa d.s
19/09/2025
Daga shafina Sani Abdullahi Wada
NAU’O’IN RUWAN FARJI DA KE NUNA AKWAI INFECTION
_________________________________
A al’ada, ruwan farji yana da bambance-bambance gwargwadon lokaci na al'ada da yanayin mace, amma idan ya sauya launi, wari, ko tsari to hakan na iya zama alamar infection.
_________________________________
GA NAU'O'IN SU KAMAR HAKA:
1. Fari mai kauri, k**ar cuku - Yana nuna fungal infection da ya hadar da candida albicans ko yeast infection.
Sau da yawa yana zuwa da ƙaiƙayi da kumburin farji.
_________________________________
2. Kore ko rawaya mai kauri - Yana nuna alamar bacterial infection ko cututtukan da ake dauka ta hanyar jima'i.
Yakan fito da wari mara daɗi.
_________________________________
3. Launin ruwan kasa ko ja ba lokacin haila ba - Na iya nuna infection, polyps, ko wasu matsaloli a mahaifa.
_________________________________
4. Fari mai kumfa ko wari - Yana iya kasancewa Trichomonas vaginalis wanda cuta ce da ake samu ta hanyar jima'i.
_________________________________
5. Launin toka ko fari mai karni - Alamar Bacterial Vaginosis (BV) ne.
_________________________________
A TAKAICE
A bisa al'ada, ruwan farji mai launin fari ko ɗan rawaya wanda baya wari, baya ƙaiƙayi wajen fitarwa shine normal ruwa da ake kira da ruwan ni'ima.
Amma duk wani ruwa da yake mai wari, launin kore, ja, ruwan kasa, mai kauri sosai ko k**ar cuku, ko mai kumfa, to wannan ba normal bane. Matsalar infection ne.
Idan kina fuskantar irin wannan, ya k**ata ki tuntuɓi likita don gwajin HVS-MCS da shan maganin da ya dace.
15/09/2025
© Sani Abdullahi Wada
16/09/2025
Ba karya farashi bane target dinsu sosuke su Dora maku talaucinda idan Zabe yazo da sun kanga maku kudi kuzabesu👌
Idan bahaka ba namiye za'a ce kayan talaka yafi kowani kaya saukin farashi a kasuwa?
Wlh akwai ranar maida biki Allah ya bamu lfy da nisan kwana Mai amfani🙏
Bismillahir Rahmanir Rahim
Assalamu Alaikum jama’ar Dandume da masoya daga ko’ina! 👋
Muna murna da bude wannan sabon shafi mai suna Dandume Forum 🌍. Wannan shafi an kirkire shi domin:
✅ Hada kan al’ummar Dandume
✅ Samar da bayanai masu amfani (ilimi, kasuwanci, kiwon lafiya, al’adu da wasanni)
✅ Wayar da kan juna da kuma kawo cigaba cikin gari
A nan, kowa yana da muryarsa. ✨ Za mu yi amfani da wannan dandalin wajen tattaunawa cikin mutunci da gaskiya, domin ganin mun kawo ci gaba ga yankinmu.
👉 Muna gayyatar ku ku bamu goyon baya ta hanyar:
Yin Like 👍 da Follow a shafi
(Share 🔄)
Da kuma bada gudummuwarku cikin tattaunawa.
Dandume Forum Inda Muryar Jama’a ke haduwa don Cigaba.
Click here to claim your Sponsored Listing.