MAN Is problem how? why?
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from MAN Is problem how? why?, Computer Company, Layin yan alewa, Lafia.
13/10/2019
J I T A - J I T A (Yada Karya)
Lallai mafi girman laifuka na harshe da musibarsa shi ne yada jita-jita, mafi yawan Jita-jita karya ce wanda ake yada ta tsakanin mutane. Kuma hakan yake haddasa rashin yarda tsakanin musulmai har a samu mummunan zato tsakanin su.
jita-jita tana aiki kamar wuta da Audiga tana fadawa KASA, GARI, ALUMMA KO GIDA ta rusa su, duk mutunci mutane da girman kasarsu in dai zasu bawa Jita-jita gurin zama za su nemi mutuncin su su rasa.
Jita-jita na haddasa rashin jituwa ta bata 'yan uwantaka ta jawo rabuwar kawuna da rashin aminci .
Jita-jita na rusa zumunci sau dayawa tana haifar da manyan laifuka sannan tana raba alaka tsakanin Abokai, ma'aurata, masoya ta rusa farin ciki ta bakanta zuciyoyi, ta bata lokaci ta haifar da asara.
Lallai Allah ya haramta taba mutuncin Musulmai
Ubangiji (SWT) Yace;
"Ya ku wadan da s**a yi imani ku nisanci mafiya yawan zato lallai sashin zato laifi ne."
"Ya ku wadan da s**a yi imani idan fasiki ya zo muku da wani babban labari to ku nemi bayani domin kada ku cuci wadansu mutane a cikin jahilci, saboda haka ku wayi gari akan abin da kuka aikata kuna masu nadama"
jita-jita masu yada ta tuni s**a sami mazauni a social media suna amfani da tunanin masu karamin tunani wajan tozarta duk wanda suke so su tozarta ko cin zarafinsa ko na iyalansa. A haka suke suke ta haifar da fitintunu ga Al'umma masu karamin tunani na musu rakiya zuwa ga halaka.
RASULULLAH (SAW) Yace;
"Duk wanda ya yada wata kalma mara kyau game da musulmi don ya bata shi da ita a duniya to ya zama hakki a kan Allah da ya narkar da shi a wuta har sai ya kawo abunda ke zartar da ita"
Allah ka tsare mu da yada Jita-jita
Jum@tMbrk & Brothers
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Lafia