Musa Abdu Shehu
Army base abuja
29/12/2025
Manyan Kalmomin Likitanci 25 da ya dace kowa ya sani da Hausa
✅Benign: Ba cutar daji ba (ba kansa ba)
✅Malignant: Cutar daji (kansa)
✅Anti-inflammatory: Magani da ke rage kumburi, zafi da radadi (misali ibuprofen, naproxen)
✅Body Mass Index (BMI): Auna kiba ta jiki bisa tsayi da nauyi
✅Biopsy: Daukar wani sashen nama domin gwaji
✅Hypotension: Hawan jini ya yi kasa
✅Hypertension: Hawan jini ya yi yawa
✅Lesion: Rauni, ciwo ko yanka a jiki
✅Non-invasive: Bincike/magani ba tare da shiga cikin jiki da kayan aiki ba
✅Outpatient: Ana shigowa asibiti a koma gida rana guda
✅Inpatient: Ana kwantar da mara lafiya a asibiti na kwana daya ko fiye
✅In remission: Cuta ta lafa ko ta tsaya, amma ba lallai ta warke gaba daya ba
✅Membrane: Siririyar fata ko nama da ke rufe ko hada sassan jiki
✅Acute: Cuta mai zuwa kwatsam, amma ba ta dade ba
✅Angina: Ciwon kirji da ya shafi zuciya, yana zuwa yana tafiya
✅Gastroesophageal Reflux Disease (GERD): Ciwon zuciya
(heartburn) / tashin acid daga ciki
✅Cellulitis: Kumburi ko kamuwa da cuta a karkashin fata
✅Epidermis: Fatar jiki ta waje
✅Neutrophils: Nau’in farin jinin jiki mafi yawa
✅Edema: Kumburi (taruwar ruwa a jiki)
✅Embolism: Toshewar jini (jinin da ya daskare)
✅Sutures: Dinki (stitches)
✅Polyp: Tsiro ko girman nama mara kauri
✅Compound fracture: Karyewar kashi da ya fito ta fata
✅Comminuted fracture: Karyewar kashi da ya tarwatse zuwa sassa da dama.
Musa Abdu Shehu
29/12/2025
Kwarai kuwa
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the public figure
Telephone
Website
Address
Lagos
ABUJA