Comrade Ibrahim
Sunana comrade Ibrahim, Dan karamin matshi Mainuna ma MATASA hanyar da zasu bi domin dogaro da kansu da kuma samun cigaba
11/09/2025
Duniya kamar madubi ce — Duk abinda kake nuna mata, hakan zata mayar maka.
Idan ka zama Mai yada alheri, zaka riski alheri. Idan rayuwarka ta cika da hassada, kage, mugunta da zalunci, to kada ka yi mamakin ganin hakan ya dawo kanka ta wata hanya da baka tapa tsammani ba.
Rayuwa tana koyar da darasi ne cikin sirri. Yana da sauƙi ka zargi kowa akan matsalarka, amma yana da wuya ka duba cikin zuciyarka ka gane cewa watakila kai ne matsalar.
Ka gyara tunaninka, ka gyara halinka, duniya zata sauya maka.
Domin duk inda aka samu matsala, akwai halayyar da s**a haifar da ita.
Ka fara nazari akan kanka.
Ka fara duba kanka kafin ka yanke ma wasu hukunci. Allah SWT yasa mufi karfin zuciyoyin mu🤲
Sunana Comrade Ibrahim✍️
10/09/2025
MATASA, Ku Farka: Kada ku Bi Siyasa Ko Addini Ba Tare da Fahimta Ba!!
A rayuwar ɗan adam, siyasa da addini su ne ginshiƙan tafiyar da rayuwa da zamantakewa. Amma babban kuskure da ake yawan tafkawa shine, bin siyasa ko addini ba tare da manufa ko fahimta ba. Wannan matsala ce da ta hana dimbin matasa da dama kaiwa ga nasara a rayuwa, kuma ta durƙusar da al’umma gaba ɗaya.
SIYASA BA TARE DA MANUFA BA:
Yau da kullum kana jin mutane suna cikin hayaniyar siyasa — suna goyon baya, suna fada, suna kashe lokaci da kuzarin su. Amma daza ka tambayi mutum: Me yasa kake goyon bayan wannan ɗan siyasar? — Bazai baka amsa mai ma’ana ba. Bai san ma manufar wanda yake bi ba, b***e kuma ya fahimci yadda zai amfana dashi.
Bin siyasa da makanta yana sa mutum ya zama kayan amfani, kayan talla, ko kayan yaƙi kawai. Ana amfani da shi wajen tada hankali, yajin aiki, ko yayata ƙarya, amma a ƙarshe ba ya amfana da komai sai da nadama.
ADDINI BA TARE DA MANUFA BA:
Haka nan a ɓangaren addini, wasu suna bin malamai ko wani rukuni na addini, ba domin su karu ko fahimta ba, sai dai kawai saboda kowa yana yi, ko wani mutum da suke girmamawa yana yi. Wannan yana haifar da ruɗani, gaba, ƙiyayya da fitina, domin dama ba don fahimta akeyi ba — sai dan son zuciya.
A addini, zaka iya ganin mutum yana ƙin ɗan’uwansa saboda ra’ayi ko mafari, ba tare da ya fahimci me addininsa ya ce ba. Wannan ba addini ba ne, ruɗani ne.
ABIN YI SHINE:
- Ka zama mai ra’ayi tare da fahimta.
- Kada ka tsaya goyon baya wani face ka fahimci manufarsa.
- Ka bi addini ne saboda ka gane gaskiya, ba kawai saboda wani ba.
- Ka rika nazari da karatu, kada kowa ya zama makaho mai ja maka hanya.
Kar a manta:
Siyasa da addini sun fi amfani idan an bi su da ilimi da hangen nesa. Idan ba haka ba, sai dai su zama hanyar rushewar mutum da lalata al’umma.
"Ka bi gaskiya, kada ka bi taron jama'a."
Kuyi sharing wannan rubutun ya Kai ga kowani MATASHI musamman matasan arewa 🙏
Sunana Comrade Ibrahim✍️
09/09/2025
Mutum yana rayuwa ne tsakanin damar da ba ta da tabbaci da kuma ajalinsa da bai san ranarta ba. Idan ka fahimci wannan, zaka daina ɓata lokaci da ƙyale kanka cikin shagala ko wasa. Ka daina jira sai ka rasa wani, ko wani abu ya faru, sannan ka gane darajar lokaci, mutane, da rayuwa.
Rayuwa ba a sake ta sau biyu. Idan ka ɓata lokacin ka yau, baka da tabbacin akan gobe. Ka rinka rayuwa da natsuwa, da tunani mai zurfi, domin duk abinda ka shuka wallahi zaka girbeshi da hannun ka
Comrade Ibrahim ✍️
09/09/2025
KU KARE KANKU DAGA TARKON 'YAN ISKA
Datti Assalafiy✍️
Wasu gungun 'yan iska suna cigaba da fadada hanyoyin da suke dana wa mutane tarko domin su mallaki hotuna da bidiyo na tsiraci
Yadda suke yi shine zasu yi kokarin neman lambar wayanka, sai su fakaici lokacin da kake online, sai kaga an kiraka video call da layin da baka sani ba
Kana amsa kiran sai ka ga mace tsirara tana wasa da nonuwanta da gabanta, to a wannan lokacin zata rinjayeka, idan ka biye mata shikenan sun samu abinda suke so
Ko baka biye mata ba indai fuskarka ya fito a bidiyon to sun samu abinda suke so, domin kafin su kiraka sai sun kunna wata software app da take recording video call
Kuna gama video call din sai su tura maka su ce ka sayi bidiyonka, daga nan sun mayar da kai ATM na ciran kudi, kungiya ne suke da shi
Sun fi yin haka da sassafe ko da dare lokacin da s**a san mutum yana gida yana hutawa, Wallahi wani ba halin sa bane neman matan banza, tsautsayi sai ya jashi ya fada, ko idan ya manta bai yi azkar ba
Idan irin wannan abin ya faru wani zai ji kamar ya kashe kansa saboda yana tsoron kar sirrinsa ya fita zai yi ta tura musu kudi, abinda ya kamata ku yi shine ku sanar da jami'in tsaro wanda ya san aiki
Don haka jama'a a kiyaye amsa kiran video call na layin da bakayi saving akan wayarka ba, hatta video call da ake kira daga Facebook da Telegram indai ba ka san wanda ya kira ba kar ka amsa
Insha Allahu zamu cigaba da bawa mutane shawarwari akan duk wani sharri na mutanen banza da suke kawowa domin su cutar da al'ummah
Ku taimaka wajen yada sakon ta sigar da ta dace domin a kare 'yan uwa daga fadawa tarkon 'yan iska karuwai
Allah Ya karemu gaba daya
09/09/2025
Rahotanni sun nuna matasa 'yan zanga-zanga sun samu nasarar kifar da Gwamnatin kasar Nepal bayan da Sojoji s**a bayyana amshe mulkin kasar na wucin gadi.
Me za ku ce?
Daga Ayau News
09/09/2025
An ce an kashe biliyan 2 kan ruwa, amma har yau jama’ar kebbi na shan ruwan kwatami? Ina aikin? Ina kudin?
Comrade Ibrahim
09/09/2025
Subhananllah
Cigiya Cigiya.....
Tun jiya ake neman sa har yanzun babu labarin sa, Ya bar gida Tungan Goro da zummar zuwa talla.
Sunan sa Mansir Bawa ɗa ne ga Sarkin Hausawa Tungan Goro dake garin Minna.
Ga wanda Allah ya ganshi ko yaji labarin sa ya tuntubi wannan lambar....07083386870
09/09/2025
MATASHI, ka tuna da wannan: kana numfashi amma baka da tabbacin har yaushe ne. Baka san ko gobe zaka mutu ba, kuma baka san ko yau ce ranar ka ta ƙarshe ba.
To me zai hana ka yi amfani da wannan damar ta rayuwa wajen aikata alheri? Ka gyara halinka, ka nemi ilimi, ka rike iyayenka da mutunci, ka tsare zuciyarka daga sharri, ka zaɓi abokai nagari, ka bar abinda bai da amfani.
Rayuwa dama ce guda daya, kuma duk wanda ya yi wasa da ita zai yi nadama a nan duniya harma da lahira. Ka rayu yau kamar wanda ba zai ga gobe ba, ka kuma ka shiryama gobe kamar wanda zai rayu tsawon shekaru.
Allah ya tsaremu da ƙarshen mara kyau, ya sa rayuwarmu ta zama abar alfahari, ba nadama ba. 🤲
Sunana comrade Ibrahim✍️
MATASA tunda munsan matsalar da muke fama da ita a arewa. Toh Mai zai hana mu hada kawunanmu don nemo mafita!!
Kana saurayi in har ka ga rarar lokaci ya yi maka yawa toh ka sani kana cikin babbar matsala.
09/09/2025
MUTUNCI!!
Mutunci shine asalin ɗan adam. Shi ne garkuwa da mutum ke amfani da shi wajen kare kansa daga tozarci, raini da kaskanci. Mutum mai mutunci, ko bai da dukiya, yana da daraja a idon mutane da kuma a wajen Allah. Idan kana da mutunci, mutane zasu girmama ka, su yarda da kai, su kuma daraja maganarka.
A yau da yawa sun sayar da mutuncinsu saboda kudi, matsayi ko bukatun duniya. Sun manta cewa dukiyar da ka samu ta hanyar kaskanci, ba zata hana su jin kunya ba. Duk darajar da aka baka saboda karya ko wulakanci, ba zata dawwama ba.
Mutunci yana farawa ne daga gida: yadda kake mu’amala da iyayenka, abokanka, makwabta da al’umma. Harshe mai kyau, gaskiya, rikon amana da kame kai — duk suna daga cikin ginshiƙan mutunci. Idan ka gaza kula da wadannan, ka rasa mutuncinka, kafin ma duniya ta kalle ka a matsayin mara mutunci.
Ka kula da mutuncinka fiye da dukiya. Saboda mutunci na iya baka abinda kudi bazasu iya siya ba: kaman yarda, amincewa, daraja da nagarta.
Ka tuna: mutuncinka shine sunanka, shine tarihin ka, shine abin da zaka bari bayan rayuwa. Kar ka sayar da shi akan abin duniya.
Sunana Comrade Ibrahim ✍️
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Minna
NIGER