Tsohon Nguru Community Development Forum
The Page Was Created To Serve Tsohon Nguru Community
03/06/2026
Tsohon Nguru Community Development Forum tana miƙa saƙon ta'aziyarta ga Vice Chairman na wannan qungiya, Babagana Mele Mai Nguru bisa rashin Kaka da s**ayi yau Laraba.
Muna addu'a Ubangiji Allah ya gafarta mata
30/05/2026
Chigiya! Chigiya!! Chigiya!!!
Muna bada chigiyar wannan yaro, yanzu haka yana gidan Ari mai unguwa a Tsohon Nguru.
Duk wanda ya san shi, sai yaje chan ya kaishi gidansu.
A taimaka Please, yaro ne ƙarami, baya faɗan ko sunansa ma, ballantana sunan mahaifansa ko unguwarsu
29/05/2026
Saƙon Taya Murna
Qungiyar Tsohon Nguru Community Development Forum tana taya Babagana Muhammad Shettima BMS, wanda shine chairman BoT na qungiyar da kuma Mallam Bashir Lawan , wanda shi kuma member ne a BoT ɗin qungiyar murnar sauƙe farali na Hajji.
Muna musu addu'a Allah ya ƙarbi ibadar da s**ayi, Allah ya dawo da su gida lafiya
29/05/2026
Nan wanne layi ne a Tsohon Nguru 👇🏿
Saka mana a comment section idan ka gane
29/05/2026
Chairman, Muhammad Sani Amadu Nguru tareda Patron na wannan qungiya, Tsohon Nguru Community Development Forum kuma ɗan takarar gomna na jam'iyyar APC na jihar Yobe, Alhaji Baba Mallam Wali
29/05/2026
MASALLACIN JUMA'A NA NATON AREWA NGURU
Yau Juma'a, 29th ga watan May aka gudanar da taron buɗe sabon masallacin juma'a a unguwar Naton Arewa dake anan Tsohon Nguru.
Sheikh Khalifa Fatihu ne ya jagoranci buɗe Masallacin wanda Shehu Muhammad Mahiru ya gina.
28/05/2026
GAYYATA! GAYYATA!! GAYYATA!!!
Ana farin cikin gayyatar ƴan'uwa musulmai zuwa buɗe Masallacin Juma'a gobe Juma'a, 29th ga watan May a Naton Arewa, gefen maƙabartar Sheikh Ngibirima dake anan Tsohon Nguru wanda Engr. Yusuf Maihaja (Garkuwa) yagina.
Sanarwa: Tijjani Abubakar
28/05/2026
Ziyarar Barka Da Zuwa
Hakimin Tsohon Nguru Ngilewa, Alhaji Zannah Mai Dala ya kaiwa Sheikh Mallam Musa Kallah ziyarar barka da zuwa da yayi daga ƙasar Egypt domin yi masa aiki.
28/05/2026
ZIYARAR GAISUWA DA BARKA DA ZUWA
Kwamishinan Ilimi Matakin Farko na jihar Yobe, Associate Abba Idris Adam ya kai ziyarar jaje da gaisuwar lafiya ga Malam Musa Kallah bayan dawowarsa daga ƙasar Egypt, inda ya je domin kula da lafiyarsa.
A yayin ziyarar, Kwamishinan ya bayyana farin cikinsa da ganin Malam Musa Kallah cikin ƙoshin lafiya bayan dawowarsa gida lafiya. Yace wannan ziyara ta nuna muhimmancin kula da juna da kuma nuna ƙauna da tausayi tsakanin al’umma, musamman ga waɗanda s**a fuskanci rashin lafiya.
Kwamishinan ya yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki ya ci gaba da ba Malam Musa Kallah cikakkiyar lafiya da nisan kwana, ya kuma kare shi daga dukkan wani rashin lafiya a nan gaba. Haka kuma ya jajanta tare da ƙarfafa masa guiwa kan muhimmancin cigaba da kula da lafiyarsa kamar yadda likitoci s**a ba shi shawara.
Shi ma Malam Musa Kallah ya nuna godiya matuƙa bisa wannan ziyara ta karamci da nuna kulawa da Kwamishinan Ilimi ya kai masa, yana mai cewa irin wannan ziyara na ƙara dankon zumunci.
✍🏿 Muhammad Adamu Malami
P.A to the Honourable Commissioner,
MOBSE YOBE STATE
28052026
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Nguru