Birnin SHEHU Reporters

Birnin SHEHU Reporters

Share

This page was created to publish news and voicer of the voiceless. As well as motivating people's

10/11/2025

Ba zamu tattauna da 'yan ta’adda ba kuma dole a samu zaman lafiya a Najeriya -Shugaba Tinubu.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa batun tsaron Najeriya ba abu ba ne da za a yi masa rangwame ko tattaunawa, yana mai cewa gwamnati ta samu gagarumin ci gaba a yaƙin da ake da ‘yan ta’adda da masu tayar da hankali a sassan ƙasar nan.

A wata sanarwa da aka wallafa a shafin X na fadar shugaban ƙasa, Tinubu ya ce gwamnatin sa ta ƙara haɗa kai tsakanin hukumomin tsaro, abin da ya kai ga damke, hallaka da kuma gurfanar da manyan ‘yan ta’adda da ke da hannu a hare-hare na baya-bayan nan.

Shugaban ya kara da cewa an ɗauki sabbin matakai na haɗin gwiwa don tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Tinubu ya ce: “Ba za mu lamunci rashin tsaro ba. Zaman lafiya dole ne — ba zabi ba ne.”

10/11/2025

Zanga zanga ta barke a fadar white house dake amurka inda amurkawa sunce doli Sai Trump ya jida bisa mulki

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Sokoto?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Address

Mabera Mujaya Opp Trade Fair Road
Sokoto