YUSIF M SALEH

YUSIF M SALEH

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from YUSIF M SALEH, Blogger, Naibawa yan Lemo market, .

22/03/2026

mata anhadu agidan lale da ki tso SE anjira hhhh😆

Photos from YUSIF M SALEH's post 10/01/2026

ASLM JAMA,A MUNA CIKI YAR KANINMU YA FITA TUN SAFE 07:30 BABU SHI BA LABARIN SA DAN ALLAH KU TEMAKA MANA DA SHARING IN ANJI LABARINSA A TUTUBI WANAN LAMBAR DAKE KASA
👉0708 235 1352
👉0810 010 0952

12/10/2025

MUTANE 10 DA YA KAMATA KA CIRE DAGA RAYUWARKA IDAN KANA SON CI GABA

Ci gaban ka a rayuwa ya dogara ne sosai akan irin mutanen da ka yarda su kewaye ka. Zaɓan abokan tafiya ba girman kai bane, KARIYA CE ga lafiyar kwakwalwarka da kuma makomarka.

Bayan dogon nazari, ga kalar mutane guda 10 da ya kamata ka nesanta kanka da su: Don ni na jima da yin hakan kuma Alhamdullilah. Ku dauki No. 4 da 5 da matuƙar Mahimmanci.. E G*y Why.

1. MAI YAWAN KORAFI: Wanda koda yaushe sai ya kawo labarin abin da ba ya tafiya daidai. Yana busar da zuciya ya kuma hana a ga alkhairi a gurare da dama na rayuwa.

2. MAI HASSADA: Wanda yake jin zafin nasararka a ɓoye, kuma baya taɓa yin farin ciki na gaskiya da kai.

3. MAI GULMA DA TSEGUMI: Wanda aikinsa shine ya kawo maka maganar wani, kuma ya kai taka ga wani. Irin wannan baya riƙe amana.

4. MAI RAUNANA GWIWA: Wanda duk lokacin da ka faɗi burinka, sai ya nuna maka dalilai 100 da yasa ba za ka iya ba.

5. WANDA BAYA SON CI GABANKA: Abokin da yake son ku zauna a wuri ɗaya. Idan ya ga kana ƙoƙarin tashi, sai ya nemi hanyar da zai jawo ka ƙasa.

6. MAI FUSKA BIYU: A gabanka abokinka ne, amma a bayan idonka maƙiyinka ne.

7. MAI JAWO RIGIMA: Wanda koda yaushe yana cikin faɗa da tashin hankali. Yana lalata zaman lafiya.

8. WANDA YAKE NEMA NA DON BUKATA KAWAI: Sai idan yana da buƙata zai neme ka, amma idan ka shiga hali, ba za ka taɓa ganinshi ba.

9. ABOKIN BANZA: Wanda aikinsa shine ya koya maka munanan ɗabi'u kamar shaye-shaye, c**a, Neman mata, da ɓata lokaci.

10. MAI YAWAN BADA UZURI: Wanda baya taɓa ɗaukar nauyin kuskurensa, koda yaushe wasu ne suke da laifi a wajensa.

A takaice, wane irin mutum ne kai ma ka yanke shawarar cirewa daga rayuwarka don samun nutsuwa?
A faɗa a comment, mu ƙaru da juna.

UMAR ALIYU DAHIRU ✍️

10/10/2025

Allhdulillahi bini imatika ya arahamarahimin

Culinary Team

Attire

Telephone

Website