DNN Hausa
DNN News Hausa: Sahihan Labarai Da Ɗumi-Ɗumi | Bincike | Siyasa | Shirye-Shirye Na Musamman | Da Labaran Wasanni Da na Nishaɗi.
23/06/2026
"Idan ba'a haɗa maka da Kuɗin masu Kidnapping ba to za'a siyar da gidan ku a karbo ka ko matar"
Sheikh Ahmad Yusuf Guruntum, Malamin Islama.
23/06/2026
Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana goyon bayan ta ga matakin gurfanar da mutane 24 da ake zargi da hannu a kisan gillar da aka yi wa wata mata a yankin Maraban Jos, tana mai cewa hakan wani muhimmin mataki ne wajen tabbatar da adalci da kuma mutunta doka.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Ahmed Maiyaki, ya fitar a ranar Talata, gwamnatin ta yabawa rundunar ‘yan sandan jihar bisa gaggawar da ta yi wajen daukar mataki kan lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’umma.
23/06/2026
Gwamnatin Amurka ta ayyana wani ɗan Najeriya tare da wasu mutane da kamfanoni a Turai, Gabas ta Tsakiya da Afirka ta Yamma a matsayin waɗanda ake zargi da taimaka wa ƙungiyar ta'addanci ta ISIS wajen gudanar da harkokin kuɗaɗen ta.
A wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar, mai magana da yawunta, Thomas Pigott, ya ce matakin ya shafi mutum uku da kamfanoni shida da ake zargi da taka muhimmiyar rawa wajen sauƙaƙa safarar kuɗaɗe domin ayyukan ISIS a sassa daban-daban na duniya.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana cikakken sunan ɗan Najeriyar ko ƙarin bayanai game da sauran mutanen da abin ya shafa ba zuwa lokacin fitar da rahoton.
23/06/2026
Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta mika takardar ta a hukumance domin ficewa daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC), watanni tara bayan sanar da wannan aniya tare da kasashen Mali da Burkina Faso.
Kotun ICC mai hedikwata a birnin Hague na kasar Netherlands ta tabbatar da cewa ta karbi sanarwar ficewar Nijar a ranar 18 ga Yunin 2026.
Tun a watan Satumban shekarar 2025 ne gwamnatin Nijar karkashin jagorancin Janar Abdourahamane Tiani, tare da Mali da Burkina Faso, s**a bayyana aniyarsu ta janye daga kotun, suna zargin ta da kasancewa wata kafa da kasashen yamma ke amfani da ita wajen nuna wariya da danniya.
A cewar ICC, ficewar Nijar ba za ta fara aiki ba sai ranar 18 ga Yunin 2027, shekara guda bayan gabatar da takardar sanarwar, kamar yadda dokokin kotun s**a tanada.
Sai dai kotun ta bayyana cewa har zuwa lokacin da ficewar za ta fara aiki, Nijar za ta ci gaba da cika dukkan sharadai da nauye-nauyen da s**a rataya a wuyan ta a matsayinta na mambar kotun.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Kano