Alfallatee

Alfallatee

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Alfallatee, Digital creator, .

11/11/2025

Episode 2

Photos from Alfallatee's post 23/10/2025

SAKON JAJANTAWA GA AL’UMMAR JIHAR NIGER

Cikin sallamawa ga hukuncin Allah Madaukakin Sarki, muke mika sakon ta’aziyya da jaje ga:

Mai Girma Gwamnan Jihar Neja, H.E. Farmer Umar Mohammed Bago;
Mai Martaba Sarkin Bida, Alh. (Dr.) Yahaya Abubakar (Etsu Nupe);
Sarkin Fulanin Masarautar Nupe, Dikko Bida;
Da kuma dukkannin al’ummar Jihar Neja, musamman mutanen Zone A, bisa mummunan hatsarin fashewar tankar mai da ya auku a kauyen Essa na Karamar Hukumar Katcha, wanda ya yi sanadin rasa rayuka masu yawa tare da jikkata wasu da dama.

Haka kuma, muna sake bayyana matuƙar bakin cikinmu da alhini game da rikicin ban tausayi da ya faru tsakanin makiyaya Fulani da al’ummar Nufawa a yankunan Gonagi da Jigi na Karamar Hukumar Edati a Jihar Neja.

Wannan mummunan lamari ya janyo rasan rayuka fiye da mutum biyar (5) Wanda s**a jikkata fiye da mutum ashirin (20), hadeda ƙonewa da rushewar gidaje sama da hamsin (50), tare da asarar dukiyoyi, dabbobi, da kayan rayuwa na al’ummomi da dama. Har yanzu, akwai wasu da ba a san inda suke ba — ko suna raye ko kuma sun rasu — abin da ya rage sai addu’a da tawakkali ga Allah Madaukakin Sarki.

Bazan iya saka wasu daga cikin hotunan anan ba saboda dokan Facebook inba haka ba da na saka maku kunga irin ta'adi da aka samu a wannan rikicin muna fatan Allah ya takaitashi.

Muna mika godiya ta musamman ga Mai Martaba Sarkin Bida, Alh. (Dr.) Yahaya Abubakar (Etsu Nupe) bisa irin matakin gaggawa da na uba da ya ɗauka, wanda ya taimaka wajen kwantar da tarzoma da hana ƙarin asarar rayuka.

Haka kuma, muna yaba da ƙoƙarin CSP Bima Enagi, D.P.O na Enagi, tare da Hakiman Gonagi da Jigi, bisa jajircewa da hangen nesa wajen daidaita lamarin tun daga farko.

Sai dai, muna roƙon Mai Girma Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Muhammad Umar Bago, da ya ɗauki matakai masu zuwa:

1. A aika da kayan tallafi da taimakon jinƙai ga waɗanda abin ya shafa, musamman iyalan da s**a rasa matsugunnansu.
2. A umarci jami’an tsaro da su gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da adalci ga waɗanda s**a mutu ko s**a jikkata.
3. A gargadi al’umma da su guji ɗaukar doka a hannunsu, domin irin waɗannan matakai na iya lalata zaman lafiya da haɗin kai da ake ƙoƙarin gina wa.
4. A ƙarfafa jami’an ’yan sanda da DSS wajen inganta tsaro da gudanar da bincike mai zurfi domin hana maimaita irin wannan mummunan lamari.

A ƙarshe, muna roƙon Allah Ya jikansu waɗanda s**a rasa rayukansu, Ya ba waɗanda s**a jikkata lafiya cikin gaggawa, kuma Ya tabbatar da zaman lafiya, fahimtar juna, da haɗin kai tsakanin dukkan al’ummomin Jihar Neja.

✍️ Khalid De General
📅 23/10/2025

20/10/2025

Allah yasa mugama da wannan duniyan lafiya

Culinary Team

Attire