Rafintofa midia

Rafintofa midia

Share

An bude wannan shafin saboda kawo muku labarai da kuma kalubalen rayuwa musamman fannin soyayya

15/07/2026

Kosai mai zafi muna bada sari

07/07/2026

Wannan Abu baiyi dadi ba

05/07/2026

Waiwaye ad on tafiya 😀

04/07/2026

MATA MASU NAUYIN BAKI: ALAMOMI 5 DA ZAKA GANE TANA SONKA KODA BATA IYA CE MAKA "I LOVE YOU

A duniyar soyayya, ba kowa ke da saukin fadin kalaman baki ba. Wasu matan suna da matukar kunya ko kuma ba su saba da kalaman soyayya na zamani ba. Idan kana tare da mace mai nauyin baki, kada ka matsa mata ta rika fada maka I love you domin soyayyarta a aikace take, ba a baki ba

Ga alamomi 5 da ya kamata maza su lura da su

1. Kula da Abincinka da (Acts of Service) Mace mai nauyin baki tana nuna soyayya ne ta hanyar hidima. Zaka ga tana tsananin damuwa da lafiyarka, abincinka, da gyaran suturarka. Idan tana yawan damuwa "Ko ka ci abinci?" ko kuma ta damu da bacin ranka, wannan shi ne asalin I love you" dinta a aikace.

2. Kishi na Boye da Kulawa ta Musamman Ba lallai ne ta iya gaya maka kalamai masu dadi ba, amma zaka fuskanci tana lura da duk wani canji a tattare da kai. Idan ta ga kana kulawa da wata, zaka ga yanayinta ya canza ko ta nuna damuwa. Kishinta yana nuna matsayinka a ranta.


3. Bada Kyaututtuka Masu Ma'ana Maimakon ta fadi kalamai, zata gwammace ta siyo maka abinda ta san kana bukata kamar turare, dinki, ko takalmi. Tana amfani da kyauta ne domin ta toshe gurbin rashin iya kalaman baki, don nuna cewa kana ranta koyaushe.


4. Saurare da Biyayya Idan kayi mata magana ko ka ba ta shawara, tana dauka da muhimmanci kwarai da gaske. Tana girmama ra'ayinka kuma tana kokarin ganin ta faranta maka rai ta hanyar bin dokokinka. A gurinta, biyayya da girmamawa sun fi kalaman soyayya na baki dadi.

5. Turo Sakonni da Daddare Ko ta WhatsApp: Idan kuna gaba-da-gaba, kunya da nauyin baki zasu hanata fadin abinda ke ranta. Amma idan ta koma gefe guda, tana iya turo maka gajeren sako na ban hakuri, addu'a, ko nuna kewarka. Rubutu yana bata damar fadin abinda baki ya kasa fada.

Nasiha ga Maza
Soyayya ba a baki take ba kawai, tana a zuciya da kuma aiki. Idan ka sami mace mai tsafta, rikon amana, da kulawa, kada ka tsane ta don kawai ba ta iya "I love you". Ka kalli ayyukanta, domin a can gaskiyar soyayyarta take.

Rafintofa midia ✍️

Telephone

Website