Arewa Web3 Labs
AREWA WEB3 LABS
Empowering Arewa minds to learn, innovate, and build in Web3. Connecting crypto enthusiasts, creators, and innovators under one hub.
To: Sir, Naziru M. Ahmad Sarkin Waka��
Sir, for your kind information and consideration.
Akwai wani hazikin matashin mawaki M S Dan Gata Musty daga garin Wudil, ya fito da wata waka, wadda ya sadaukar domin Sarkin Waka, Naziru Ahmad.
Lallai wannan waka ta fito fess, an zuba ta da hikima, basira, da GASKIYA, waka ce da ke ɗauke da saƙo mai zurfi.
Ni kaina ba mawaki ba ne, amma a gaskiya ba zan iya boye abin da na ji ba. Wannan waka ta burge ni matuƙa, domin an yi ta ne cikin ladabi, girmamawa, da fahimtar martabar Sarkin Waka.
Yakamata a yaba wa wannan matashi, a kuma ƙarfafa ma shi gwiwa, domin irin wannan ƙoƙari shi ke ɗaga darajar waka da al’adarmu gaba ɗaya.
ina fatan za ka ga wannan bidiyo ka saurara, domin waka ce da aka yi maka da zuciya ɗaya, ba kwaikwayo ba.
Allah yakara basira, ya ƙara ɗaukaka, ya kuma buɗe wa wannan matashi ƙofofin alheri. �
Click here to claim your Sponsored Listing.