MADIK ADAM
Madik adam
*KA TUNA LAHIRARKA* – 006.
*Ya kai bawan Allah!* Ka sani cewa duk wani taimako daka bayar domin addinin Allah ko domin wani bawan Allah mai buƙata – ba ya bacewa a wajen Ubangijinka. Allah yana cewa:
"إِن تَنصُرُوا اللَّهَ يَنصُرْكُمْ وَيُثَبِّتْ أَقْدَامَكُمْ"
*(Idan kun taimaki Allah, zai taimake ku, )* — ma'ana idan kun taimaki addinin Allah, to Allah zai taimake ku
Wannan ayar hujja ce a gare ka cewa, taimako ga addini ba taimako bane ga wani mutum kai tsaye, taimako ne kai tsaye ga addinin Allah.
*Ka taimaka da dukiyarka, lokacinka, ƙarfinka, iliminka, ko koda da kalma ɗaya ce mai amfani.* Domin hadisin Manzon Allah (SAW) yana cewa:
*"Allah yana taimakon bawa matuƙar bawan yana taimakon ɗan uwansa."* — Muslim
*Ya kai mai hankali!* Ka duba halin da al’umma ke ciki: masallatai ba su da wuta, almajirai suna barci da yunwa, wasu na asibiti ba su da magani, wasu iyaye ba su da abincin safe. Shin ka tsaya ka yi tunani cewa wata rana kai ne za ka iya zama cikin irin wannan hali ?
*To me ya hana ka yi tanadi tun yanzu ?* Sadaka tana hana bala’i, tana tsawaita rai, tana janyo rahamar Allah.
Manzon Allah (SAW) ya ce:
*"Ku tsare kanku daga wuta ko da da rabin dabino."* — Bukhari & Muslim
Idan rabin dabino ka iya kare ka daga wuta, to ya ya halin wanda ya gina rijiya? Ko yasa wuta a masallaci ? Ko ya biya magani ga marar lafiya ? Ko ya tallafa da Qur’ani ko ilimi ?
*Wallahi ka fi kowa buƙatar alherin da kake yiwa wasu a lahira.*
*Ka tuna lahirarka,* ka gyara tsakanin ka da Allah da mutane. Kada kayi wasa da damar da Allah ya baka yanzu. Rayuwa ba ta da tabbaci, kowa yana tafiya.
Allah ya sa mu dace da aikin alkhairi, ya sanya mu cikin masu taimakon addininsa da bayinsa.
Amin.
*Darul Khair Foundation*
Domin ayyukan saka solar a masallatai da kuma hada bohol da taimakon bayin Allah marasa lafiya da sauran ayyukan Alkhairi.
_Yaku bayin Allah kowa ya bada nasa taimakon domin a daukaka addinin Allah_
Account number- 0067204486
Bank Union bank
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Wuse