Arewa News Update

Arewa News Update

Share

“Arewa News Update shafi ne da ke kawo muku sabbin labarai daga Arewacin Najeriya da ma duniya cikin

07/06/2026

Alhamdulillah barkan mu da sake saduwa A wannan Rana ta 7 jun 2026 Insha Allah wannan Shafi na Arewa News Update zai ci gaba da kawo muku Nagartattun Labarai da Fadakarwa harma da Nishadi kuci gaba da kasancewa damu

Arewa News Update Na tare daku mun gode.

20/05/2026

Muna ci a Taya magoya bayan kungiyar Arsenal murna lashe kofin gasar premier league up up up Arsenal???

wanne fata kuma kukewa Arsenal A gaba

.

12/05/2026

Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi'u musa kwankwaso ya bayanan A wata fira da'akayi dashi cewa yarsa ce tace yabi pita obi ya masa mataimakin shugaban kasa

labarin da yake faruwa yanzu ya saka mabiya da yawa cikin wasi-wasi Akan mafitar Al'umma da Arewa shine A gaban Sanata kwankwaso ko Kuma Ra'ayin yar sa ????

zamu kawo muku cikakken Rahotan

ku ci gaba da kasance wa da Shafin Arewa News Update domin samun labarai da DUMI-DUMI 🔥🔥🔥

.

11/05/2026

KALLO YA KOMA SAMA

wata babbar kotun jihar Kano ta haramtawa jarumar fina-finan KANY WOOD Rashida Mai sa'a yin post A social media har sai Angama Shari'a

kunshin Tuhumar shine Rukayya dawayyace ta shigar da Rashida Mai sa'a karar bisa zargin bata mata sunan zargin da Ita Rashidar ta musanta

A zaman kotun na yau 11-5-2026 kotun Majistare Mai lamba 7 karkashin jagoranci Mai Shari'a Halima wali taba da belinta

sharadin belin: gabatar da Dan majalissa Mai ci da Kuma dan uwanta Wanda ya mallaki Naira miliyan 300.

'a wood.

11/05/2026

🕋 INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN
Hukumar National Hajj Commission of Nigeria ta tabbatar da rasuwar wata mahajjaciya ‘yar Najeriya a ƙasar Saudi Arabia yayin gudanar da aikin Hajjin bana.
Marigayiyar, Malamma Aishatu Muhammadu, mai shekaru 73 daga jihar Adamawa State, ta rasu ne a yayin aikin Hajji kamar yadda jami’ai s**a tabbatar.
Rahotanni sun ce marigayiyar ta fito ne daga ƙaramar hukumar Gombi, kuma hukumomi sun bayyana cewa ana ci gaba da kula da sauran mahajjatan Najeriya domin tabbatar da lafiyarsu.
Allah ya jiƙanta da rahama, ya gafarta mata kura-kuranta, ya sanya Aljannatul Firdausi ce makomarta. Allah kuma ya bai wa iyalanta da al’ummar jihar Adamawa haƙurin jure wannan rashi. 🤲

09/05/2026

ALLAHU AKBAR : Rai bakon duniya A yau Sanata Aisha jummai Alhasan (maman Taraba) take cika shekaru 5 da Rasuwa

fitachchiyar yar siyasa ce Ajihar Taraba wacce kafin Rasuwar ta tayi Takarar gwamnan Ajihar Taraba

Allah ya gafarta mata da sauran Yan uwa musulmi.

08/05/2026

HARIN ‘YAN TA’ADDA A BORNO!
Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ake zargin mayakan Islamic State West Africa Province sun kai hari kan sansanin sojoji a ƙaramar hukumar Magumeri da ke Borno State.
An ce harin ya yi sanadin rasuwar sojoji biyu tare da jikkata wani babban kwamandan soja.
Lamarin ya sake tayar da hankula kan matsalar tsaro da ake ci gaba da fuskanta a yankin Arewa maso Gabas, duk da ƙoƙarin jami’an tsaro wajen daƙile ayyukan ‘yan ta’adda.
Allah ya jiƙan waɗanda s**a rasu, ya bai wa waɗanda s**a jikkata lafiya. 🤲
👉 Mene ne ra’ayinka kan yadda za a kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin?

07/05/2026

SHARI’AR EL-RUFAI TA SAKE DAWOWA KOTU!
Tsohon gwamnan jihar Kaduna State, Nasir El-Rufai, ya sake bayyana a gaban babbar kotun tarayya da ke Kaduna domin ci gaba da sauraron shari’ar da ake yi masa kan zargin cin hanci da kuma amfani da mukami ba daidai ba.
Rahotanni sun bayyana cewa hukumar Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission ce ke tuhumar tsohon gwamnan, yayin da shari’ar ke jan hankalin jama’a da dama a fadin Najeriya.
An kuma tsaurara matakan tsaro a harabar kotun yayin ci gaba da zaman shari’ar.
👉 Shin kana ganin za a gudanar da wannan shari’a cikin adalci?

Want your business to be the top-listed Media Company in Zaria?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address

Kaduna
Zaria