Pi Pro Arewa
Pi network👇👇👇
https://t.me/+F54iCR-DE7BhMzk8
07/10/2025
A trading kana bukatar focus da kuma real experience na abunda kake baka ta tsilla-tsilla tsakanin different market ba, alhali bakada kwarewa na azo agani.
Misali kafara koyan crypto kawai sai kaji ai anasamun kudi sosai da forex, sai ka watsar da crypto kadawo forex, can sai kaji ai "degen" sunfi volatility sai ka bar forex din kakoma trading degen. Ka ga kai baka sa mu daya da katabbatar ka iya ba, kana raba hankalinka, sai kazama babu focus, ba determination, sai kaga mutum yana ta circle a gu daya bai samu abunda yake so ba.
Dole mutum yayi hakuri for the first time ya iya market daya kafun yace zai fara raba hankalinsa nanma in yana so kenan. Being versatile is good but a farkon farawanka katsaya guri daya shiyafi.
03/10/2025
Technical Analysis 101
Candlestick (8)
CANDLESTICK TIME-FRAMES
menene timeframe
Time-frame na nufin zaɓaɓɓan lokaci da aka keɓe don gudanar da wani abu. Misali, kana zuwa makaranta kullum, yayin da duk ka je makarantar kana rubuta lokacin da duk wani malami ya shigo ajinku. Bayan shekara ɗaya sai ka buɗe littafinka ka duba a wata rana a daidai wani lokaci wanne malami ne ya shigo ajinku. Wannan ranar da ka zaɓa domin bincika malamin da ya shiga a jikinku a daidai lokacin shi a kekira da "Time-frame"
Time-frames a candlestick chart jerin lokuta ne da mai gudanar da technical analysis zai zaɓi lokacin da ya ke son gudanar da binciken domin sanin tafiyar da farashi ya yi a wannan lokacin.
Idan ka zaɓi 5m time-frame to kana son ganin yadda farashi ke tafiya a cikin mintuna biyar ne, idan ka zaɓi 15m time-frame to kana son ganin yadda farashi ke tafiya a cikin mintuna sha biyar, idan ka zaɓi 1h timeframe to kana son sanin yanayin motsawar farashi na awa ɗaya, idan ka zaɓi 4h time-frame to kana son ganin yadda farashin ke tafiya na awa huɗu, idan ka zaɓi 1day time-frame to kana son ganin tafiyar da farashi ke yi a kwana ɗaya, idan ka zaɓi 1Week time-frame to kana son kasan tafiyar da farashin ke yi a sati ɗaya, idan ka zaɓi 1M time-frame to kana son ka ga yadda farashin coin ɗin ke tafiya ne a cikin wata daƴa. Ya dai danganta da irin salon kasuwancin da kake yi da kuma time-frame ɗin da kake son gudanar da bincikenka a kai.
Idan ka sanya 30M a timeframe naka to hakan yana nufin duk 1 candlestick yana bayyana bayan minti 30
Idan ka haÉ—e guda 2 zasu baka 1 hour candlestick k**ar yadda yake a hoton nan
Bullish engulfing aka samu a 30M
Da aka mayar dashi kuma 1 hour sai muka samu hammer wanda itama alamace ta bullish trend
10/09/2025
Technical Analysis 101
Candlestick (4)
Single candlestick
Shooting star 1
Mene ne Shooting star?
Amsar:
Shidai Shooting star candlestick, wani candlestick ne Wanda yake identifying reversal, ma'ana yana nuni da cewa token yana shirin faduwa.
Shidai Shooting star candlestick ana samunshi ne a saman uptrend,
Ma'ana yayin da token ya hau sosai.
Sannan kuma bayyanarshi a saman uptrend shine zai saka mai analysis yasan cewa za'a samu potential price reversal zuwa downtrend.
Shidai wannan candle din yana iya fitowa a kaloli guda 2 ,
Yakan iya fitowa da koren kala (green)
Mafi akasari kuma Jan kala (red).
Amma fitowarshi da Jan kala(red) hakan yafi tabbatar da cewa eh akwai bearish Reversal din. Ma'ana farashin yana gab da faduwa.
Shidai akan sameshi ne yayin da masu siyan token s**ayi pumping din wani coin. Hakan zai jawo hankalin masu riqe dashi su fara siyarwa har selling pressure ya hau kan token din,
Yayin da selling pressure ya hau kan token sai shi kuma candlestick na Shooting star sai ya fito, domin yin nuni ga mai analysis ko kuma masu siya cewa coin din yana gab da faduwa.
Shidai Shooting star akwai wasu abubuwa da masu analysis suke amfani dashi wajen tabbatar da analysis din da s**ayi akanshi.
Tun daga samun confirmation na trading volume, Wanda idan har idan har aka samu high trading volume yayinda Shooting star ya fito, hakan na qara tabbatar da akwai potential bearish a ksw.
Sannan ana iya amfani da technical indicators irinsu Relative strength index (RSI), domin gane qarfin strength na signal dinshi.
Sannan ana iya amfani da trendlines irinsu support level ko kuma resistance level sbd tabbatar da an samu accurate result.
A taqaice kenan akan Shooting star candlestick.
Hoton Shooting star yana qasa.
07/09/2025
Technical Analysis 101
Candlestick (3)
Wajen yin Technical Analysis a Crypto ko a sauran Financial Markets, idan mutum ya fahimci Candlestick Psychology to zai rinka kallon Chart ne k**ar yana kallon live fada tsakanin Buyers da Sellers, zai rinka fahimtar exact abinda yake faruwa a bayan fage daga duka bangarorin biyu na Buyers da Sellers saboda Candlestick ba ya taba yin karya, kuma wanda yasan Candlestick Psychology baya bukatar dole sai ya haddace Candlestick patterns irinsu Hammer, Shoo*ting Star da sauran su.
Candlestick Anatomy daban, Candlestick Psychology daban.
💎Candlestick Anatomy shine abinda aka fi sani wato siffofi da ma'anoni na sassan ji + kin Candle irinsu Upper and Low Shadow (Wick), Body, Opening price, Closing price, High da Low k**ar dai yanda yake a hoton nan.
💎 Candlestick Psychology kuma shine sakon da Candle yake isarwa ga Trader ta cikin siffar da Candle din ya bayyana da ita, inda yake bayanin yanda abubuwa s**a wakana tsakanin Buyers da Sellers, Shi Trading k**ar fada ne tsakanin Buyers da Sellers, idan Buyers s**a rinjayi Sellers sai kasuwa ta rinka tashi, idan kuma Sellers ne s**a rinjayi Buyers sai kasuwa ta rinka faduwa, wanda bai san Candlestick Psychology ba bazai iya fahimtar sakon da Candles suke isarwa ba wanda kuma da wannan ake anfani as price action ayi hasashen me zai biyo baya na tashi ko faduwar kasuwa.
💡Duk Candle guda daya yana nuna abinda ya faru a tsawon lokacin daka saka a TimeFrame dinka, a 1 Hour TimeFrame duk Candle daya yana nuna abinda ya fara na tsawon awa daya. Sannan ba'a yankewa kowane Candle hukunci har sai ya rufe Completely.
~ Candlestick Psychology yana da dan fadi amma bari muyi kadan yau sai mu dora daga baya dan kada rubutun yayi tsayi. Ga kadan daga ciki:
1. Idan kaga Jan Candlestick 🟥 to hakan yana nufin farashin da ya rufe dashi bai kai farashin daya fara dashi ba, kasuwa ta fadi kenan, Sellers sun fi rinjaye. Haka idan kaga koren Candle🟩 to hakan yana nufin farashin daya rufe dashi y
Click here to claim your Sponsored Listing.